APC: Dan majalisan Arewa da ake zargi da badakalar kudin Korona ya rasa tikitin tazarce

APC: Dan majalisan Arewa da ake zargi da badakalar kudin Korona ya rasa tikitin tazarce

  • Dan majalisa a jihar Benue ya rasa kujerar tazarce bayan da ya bar jam'iyyar Labour ya koma APC mai mulkin kasar nan
  • Dan majalisar dai shi ne ake zargi da karbar kudin 'yan mazabarsa da saunan zai sama musu tallafin Korona
  • Ya zuwa yanzu, a jihar Benue 'yan majalisu 4 kenan suka rasa tikitin komawa takara a zaben 2023 mai zuwa

Benue - Godday Odagboyi, dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Apa/Agatu, ya sha kaye a yunkurinsa na sake tsayawa takara a zaben 2023 mai zuwa, TheCable ta ruwaito.

Odagboyi wanda ya tsaya takarar neman tikitin takarar Sanata na jam’iyyar APC ya sha kaye a hannun Adama Adama, hamshakin dan kasuwa wanda aka fi sani da Otalaka.

Dan majalisa ya rasa tikitin komawa takara a jam'iyyar APC
Sauka lafiya: Dan majalisar da ake zargi da cinye tallafin Korona ya rasa tikitin tazarce | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Da yake sanar da sakamakon a ranar Asabar, shugaban kwamitin zabe Franklin Shagbaor, ya ce Adama ya samu kuri’u 21,747 inda ya doke Odagboyi wanda ya samu kuri’u 3,151.

Kara karanta wannan

Ayu ga Tambuwal: Kai ne gwarzon babban taron jam'iyyar PDP

Odagboyi dai ya lashe zaben mazabun ne a jam’iyyar Labour a 2019, amma daga baya ya koma APC a watan Yuni 2021.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A farkon watan ne mazauna mazabar suka kai kararsa ga hukumar yaki da rashawa ta EFCC da ICPC bisa zarginsa da badakala, kamar yadda Legit.ng ta tattaro.

Ana zargin dan majalisar da wasu daga cikin mataimakansa da karbar kudade daga yan mazabarsu da suka nemi cin gajiyar rancen Korona.

Mazauna yankin sun bukaci hukumomin da su binciki wadanda ake tuhuma kan zargin cewa sun bukaci jama'a da su biya kudi kafin su sami rancen.

Kayen da Odagboyi ya samu ya kawo adadin ‘yan majalisar da suka yi rashin nasara a zaben fidda gwanin da aka gudanar a Benue zuwa hudu.

Sauran wadanda suka sha kaye a zaben su ne Mark Gbillah, Francis Agbo, da Kpam Sokpo duk a karkashin jam'iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Dan takarar gwamnan APC ya fice daga jam’iyyar, ya ce sai ya yi takara a 2023

EFCC: Babban dalilin da ya sa muka kwamushe tsohon gwamnan Zamfara

A wani labarin, hukumar EFCC, ta yi bayani kan dalilin da yasa ta kame tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari.

Hukumar ta ce ta kama Yari ne bisa zarginsa da hannu a badakalar Naira biliyan 84 da ake zargin tsohon Akanta Janar na Tarayya, AGF, Ahmed Idris dashi.

Wata majiya mai karfi a hukumar ta EFCC ta bayyana hakan ne ga kamfanin dillancin labaran Najeriya a ranar Lahadi a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel