Gwamna Wike: Da Na So, Da Na Tarwatsa Jam'iyyar PDP a Daren Asabar, Hakuri Kawai Nayi

Gwamna Wike: Da Na So, Da Na Tarwatsa Jam'iyyar PDP a Daren Asabar, Hakuri Kawai Nayi

  • Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya ce da ya so, da ya tarwatsa jam'iyyar PDP a daren Asabar yayin zaben fidda gwani da aka yi
  • Gwamnan ya ce hakuri kawai yayi kuma baya son abinda zai kawo cikas ga jam'iyyar amma an yi ba daidai ba a wurin
  • Wike ya koka kan yadda aka bai wa Tambuwal fili a karo na biyu inda ya bayyana janyewarsa tare da cewa magoya bayansa su zabi Atiku

Rivers - Gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers a ranar Litinin ya ce da ya so, da ya tarwatsa jam'iyyar PDP a ranar Asabar yayin zaben fidda dan takarar shugabancin kasa a ranar Asabar, amma sai bai yi hakan ba.

An yi zaben fidda dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar domin zaben 2023 mai zuwa.

Kara karanta wannan

Na Yi Matuƙar Takaicin Yadda Daliget Ɗin Jihar Mu Ba Su Zaɓe Ni Ba, Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Na PDP

Da Na So, Da Na Tarwatsa Jam'iyyar PDP a Daren Asabar - Gwamna Wike
Da Na So, Da Na Tarwatsa Jam'iyyar PDP a Daren Asabar - Gwamna Wike. Hoto daga Premiumtimesng.com
Asali: UGC
"Da na so tarwatsa taron, da na yi hakan kuma na sanar da su. Akwai mutanen da za ka yi zaton 'yan Adam ne, amma ba mutane ba ne," yace.

Premium Times ta rahoto cewa, Wike ya sanar da hakan a wani biki da aka shirya a Fatakwal domin taya shi murnar dawowa gida daga zaben fidda gwanin inda Atiku Abubakar ya lallasa shi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ban taba ganin inda mutane ke saba doka ba da tsarika. Wani ya yi magana, a wannan lokacin ne kadai ya ke magana kan cewa ya janye. Ba a kira shi ba," Gwamnan Rivers ya fada yayin da ya ke nufi da gwamnan jihar Sokoto kuma dan takara, Aminu Tambuwal, wanda ya janye daga takarar kuma ya bukaci magoya bayansa da su zabi Atiku.
"Kawai na yanke shawarar cewa jam'iyyar mu ba za ta tarwatse ba. Da sai na bar inda na ke zaune kuma in ce ba za a cigaba da wannan zaben har sai an bar ni nayi magana. Da sai na baje shi warwas."

Kara karanta wannan

Bayan ya gaza samun takara, Gwamna Wike ya fallasa abin da ya faru a zaben PDP da 2019

Gwamna Wike ya juye fushinsa kan shugabannin jam'iyyar da suka bar gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, ya yi magana karo na biyu bayan cinye lokacin da aka bai wa kowanne dan takara domin jawabi ga deliget.

Tambuwal yayin jawabinsa karo na biyu ga deliget, ya sanar da janyewar shi daga takarar kuma ya ce su zabi Atiku. Wannan cigaban, Wike yace ya saba dokar taron da tsarikansu.

Masu kiyasin siyasa sun sakankance cewa Wike zai iya samun kuri'u masu yawa har ya yi caraf da tikitin da Tambuwal bai janye ba.

A bidiyon da aka dauka a ziyarar da ya kai wa gwamnan Sokoto, Shugaban PDP, Iyorchia Ayu, an ji yana kambama Tambuwal inda ya ke kiransa da sarkin taron.

Abubakar mai shekara 75 ya samu kuri'u 371 inda yayi caraf da tikitin takarar shugabancin kasa, yayin da Wike ya zo na biyu bayan samun kuri'u 237.

Bukola Saraki, tsohon shugaban majalisar dattawa, ya zo na uku inda ya samu kuri'u 70 yayin da gwamnan Akwa Ibom,Udom Emmanuel ya zo na hudu da kuri'u 38.

Kara karanta wannan

Ba zan yi amai na lashe ba: Martanin gwamna Wike da ya sha kaye bayan ganawa da Atiku

Duk da jawabin Wike ya bayyana cewa yana goyon bayan Abubakar da PDP a zabe mai zuwa, an gano ya matukar fusata da abinda ya faru.

Bayan ya gaza samun takara, Gwamna Wike ya fallasa abin da ya faru a zaben PDP da 2019

A wani labari na daban, a ranar Litinin aka ji Nyesom Wike yana zargin abokan aikinsa daga yankin kudancin Najeriya da taimakawa wajen rashin nasarar da ya samu a PDP.

Jaridar This Day ta rahoto Nyesom Wike yana mai cewa amfanin takararsa shi ne ya nunawa yankin Arewa cewa 'yan kudu su na da karfin da za su iya takara.

Da yake jawabi a garin Fatakwal a taron da aka shirya domin tarbarsa bayan zaben fitar da gwani, Wike ya ce na-kusa da Atiku ba su da wani nauyi a mizanin siyasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel