Da Ɗuminsa: Kotu Ta Ƙwace Kujerun Ƴan Majalisa 16 Saboda Ficewa Daga PDP

Da Ɗuminsa: Kotu Ta Ƙwace Kujerun Ƴan Majalisa 16 Saboda Ficewa Daga PDP

  • Babbar Kotun Gwamnatin Tarayya da ke Abuja ta kori ‘yan majalisar Jihar Ebonyi 17 wadanda suka sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC
  • A ranar 17 ga watan Nuwamban 2020, ‘yan majalisar suka bar jam’iyyar zuwa jam’iyya mai mulki tare da gwamnan jihar, David Umahi da mataimakin sa, Dr Eric Kelechi
  • Alkalin kotun, Justice Inyang Ekwo ya yanke hukunci akan yadda ‘yan siyasar suka bar jam’iyyar da ta dauki nauyin su, don haka yace ba za su iya wucewa da kuri’un ta zuwa wata ba

FCT, Abuja - A ranar Talata, babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta kori ‘yan majalisar Jihar Ebonyi guda 17 wadanda suka bar PDP zuwa jam’iyyar APC, daga mukaman su, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Karin bayani: PDP ta mika sunayen masu maye gurbin gwamnan APC da mataimakinsa da aka tsige ga INEC

A ranar 17 ga watan Nuwamban shekarar 2020, Gwamna David Umahi da mataimakin sa, Dr Eric Kelechi Igwe suka koma APC.

Da Ɗuminsa: Kotu Ta Ƙwace Kujerun Ƴan Majalisa 16 Saboda Ficewa Daga PDP
Da Ɗuminsa: Kotu Ta Kori Ƴan Majalisa 16 Saboda Ficewa Daga PDP a Ebonyi. Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A hukuncin da kotu ta yanke bisa alkalancin Justice Inyang Ekwo, ta yi nazari akan yadda ‘yan majalisar suka bar jam’iyyar da aka zabe su zuwa wata, hakan yasa kotu ta hana su komawa wata jam’iyyar da kuri’un wata.

Kamar yadda Vanguard ta rahoto yadda alkalin ya yanke hukuncin, ‘yan majalisar sun hau kujerar ne lokacin suna PDP, don haka ba za su wuce wata jam’iyyar ba da kuri’un ta.

Doka ne sauka daga mukamin

Kamar yadda kotu ta yi hukunci da sashi na 109(1) (g) na kundin tsarin mulkin 1999 akan kada a bayar da dama ga ‘yan majalisa idan sun sauya sheka har sai sun warware zare da abawa.

Kara karanta wannan

‘Yan siyasa 9 da za su iya asarar kujerunsu a kotu a sakamakon sauya-sheka zuwa APC

Kotun ta tsaya akan cewa lallai PDP ce ta daura su akan mulki.

Ta kuma bayar da umarni akan su yi gaggawar sauka daga kujerun su kuma su dakata daga yin kai-komo a matsayin ‘yan majalisar Jihar Ebonyi.

Don haka kotu ta bayar da umarnin ga hukumar zabe mai zaman kanta, INEC akan ta ba PDP damar kawo jerin sunayen ‘yan PDP da zasu maye gurbin korarrun sannan ta ba su shaidar hawa mukaman su.

Wajibi ne su biya duk albashin da aka biya su tun daga sauya shekar da suka yi

Kotu ta ce a madadin hakan INEC za ta iya shirya wani zaben cikin kwana 90 wanda za a yi a Jihar Ebonyi don samun masu maye gurbin su.

Har ila yau, ta ba su umarnin mayar da albashin da aka dinga biyan su tun daga lokacin da suka sauya shekar zuwa APC har zuwa yanzu.

Kara karanta wannan

Tsige gwamnan Ebonyi: Shehu Sani ya bayyana abun da zai faru da sauran gwamnonin da suka sauya sheka

2023: Ƙungiyar musulmai ta buƙaci Gwamna Ugwuanyi ya fito ya nemi kujerar Buhari

A wani rahoton, kungiyar hadin kan al’ummar musulmi, UMUL ta bukaci dan kabilar Ibo ya tsaya takarar shugaban kasa idan 2023 ta zo, The Sun ta ruwaito.

Kungiyar ta musulmai ta ce lokaci ya yi da cikin yankuna biyar da ke kasar nan, ko wanne yanki zai samu adalci da daidaito da juna, hakan yasa take goyon bayan Igbo ya amshi mulkin Najeriya.

Kamar yadda kungiyar ta shaida, dama akwai manyan yaruka uku a Najeriya, Hausa, Yoruba da Ibo, don haka in har ana son adalci, ya kamata a ba Ibo damar mulkar kasa don kwantar da tarzomar da ke tasowa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel