2023: Ƙungiyar musulmai ta buƙaci Gwamna Ugwuanyi ya fito ya nemi kujerar Buhari

2023: Ƙungiyar musulmai ta buƙaci Gwamna Ugwuanyi ya fito ya nemi kujerar Buhari

  • Kungiyar hadin kan al’ummar musulmai, UMUL ta arewacin Najeriya ta goyi bayan dan kabilar Ibo ya yi shugabancin kasa a shekarar 2023
  • Kungiyar ta ce lokaci ya yi wanda ko wanne yanki cikin yankuna 5 da ke Najeriya zai samu adalci da daidaito, hakan yasa take goyon bayan Ibo ya mulki Najeriya
  • Kamar yadda kungiyar ta yi bayani, cikin manyan yarukan da ke Najeriya, Hausa da Yoruba duk sun yi mulki, don haka zai fi kamata a ba ‘yan yankin gabashin kasar nan dama

Kungiyar hadin kan al’ummar musulmi, UMUL ta bukaci dan kabilar Ibo ya tsaya takarar shugaban kasa idan 2023 ta zo, The Sun ta ruwaito.

Kungiyar ta musulmai ta ce lokaci ya yi da cikin yankuna biyar da ke kasar nan, ko wanne yanki zai samu adalci da daidaito da juna, hakan yasa take goyon bayan Igbo ya amshi mulkin Najeriya.

Kara karanta wannan

Tsufa labari: Tsohuwa mai shekaru 102 ta fito haikan, ta ce ita zata gaji Buhari a 2023

2023: Ƙungiyar musulmai ta buƙaci Gwamna Ugwuanyi ya fito takarar shugaban ƙasa
2023: Ƙungiyar musulmai ta buƙaci Gwamnan Enugu ya fito takarar shugaban ƙasa. Hoto: The Nation
Asali: UGC

Kamar yadda kungiyar ta shaida, dama akwai manyan yaruka uku a Najeriya, Hausa, Yoruba da Ibo, don haka in har ana son adalci, ya kamata a ba Ibo damar mulkar kasa don kwantar da tarzomar da ke tasowa.

Kungiyar ta yi wannan bayanin ne ta wata takarda wacce shugaban kungiyar na kasa, Mallam Abubakar Mustapha, Sakataren kungiyar, Sheikh Sanda Almisry da kuma sakataren watsa labaran kungiyar, Mallam Jamil Arafat suka sanya hannu.

Kungiyar ta bayyana yadda ya kwantar da wata tarzomar addini a shekarar da ta gabata a Nsukka

The Sun ta nuna yadda takardar ta shaida cewa:

“Kamar yadda kowa ya san kungiyar mu ta addini ce wacce take kawo hadin kai da ci gaba a kasa, mun yanke shawarar bin bayan Ibo ya mulki kasar nan da fatan masu rajin kafa kasar Biafra zasu dakata cikin gaggawa.

Kara karanta wannan

IBB ga 'yan siyasa: Kar ku yi wasa da hadin kan 'yan Najeriya

“Dalilin hakan ne yasa muka zabi tsohon dan majalisar wakilai kuma gwamnan Jihar Enugu, Chief Ifeanyi Ugwuanyi, “Gburugburu”, a matsayin shugaban da ya ke kawo hadin kai a yankin kudu maso gabas, mun yarda ya fito ya tsaya takara.
“Najeriya tana cikin tashin hankali don haka take bukatar shugaba na kwarai wanda yake da tarihi mai kyau dangane da ilimin tattali don tabbatar da ya ciyar da ko wacce jihar da ke kasar nan gaba.”

Kungiyar ta ce ta yi amanna da gwamnan dari bisa dari

Takardar ta ci gaba da bayyana yadda a tarihi gwamnan Enugu ne kadai gwamnan da ya yi aiki da kiristoci da musulmai kuma duk suka hada kai suna zaman lafiya.

Ta kara da tunatar da yadda Gwamna Ugwuanyi ya yi gaggawar tura jami’an tsaro Nsukka a shekarar da ta gabata don dawo da zaman lafiya bayan barkewar rikicin addini duk da an lalata masallatai biyu a lokacin, sai da gwamnan ya tabbatar ya kara gina wa musulman yankin masallatan.

Kara karanta wannan

2023: Wata Ƙungiya Ta Sake Shawartar Atiku Ya Haƙura Da Batun Sake Fitowa Takarar Shugaban Ƙasa

A cewar kungiyar, ta amince dari bisa dari da Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi, kuma ta tabbatar da cewa in har aka zabe shi zai yi amfani da salon mulkin da ya yi a Jihar Enugu wurin kawo zaman lafiya, hadin kai, tsaro da kwanciyar hankali a Najeriya.

Buhari: Na Ji Daɗin Yadda Masu Hannu Da Shuni Suka Gane Cewa Canja Najeriya Ba Aikin Mutum Ɗaya Bane

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ya yi farin cikin sanin cewa kusoshin Najeriya sun gane cewa canja kasar nan aikin kowa ne, The Cable ta ruwaito.

Kamar yadda kakakin shugaban kasa, Femi Adesina ya bayyana a wata takarda, Buhari ya yi wannan furucin ne a ranar Lahadi a wata liyafa ta girmama shugabannin kwamitin kasuwanci, siyasa, kafafen watsa labarai da sauran ma’aikata.

Dama a watan Janairun 2021 The Cable ta bayyana yadda Buhari ya zargi masu fada a jin kasar nan da kawo cikas ga gwamnatin sa.

Kara karanta wannan

2023: Tsohon Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa, Salisu Tanko, Ya Goyi Bayan Shugabanci Ya Koma Kudu

Asali: Legit.ng

Online view pixel