‘Yan siyasa 9 da za su iya asarar kujerunsu a kotu a sakamakon sauya-sheka zuwa APC

‘Yan siyasa 9 da za su iya asarar kujerunsu a kotu a sakamakon sauya-sheka zuwa APC

  • Babban kotun tarayya mai zama a Abuja ta sauke Gwamnan Ebonyi, Dave Umahi daga kujerarsa
  • Haka zalika Alkali ya sauke mataimakinsa, Eric Igwe da shugaban majalisar jihar saboda barin PDP
  • Akwai wasu ‘yan siyasa da-dama da suka canza sheka zuwa APC da za su iya rasa kujerunsu a kotu

Bayan hukuncin da Alkali ya zartar, Daily Trust ta kawo jerin wasu ‘yan siyasa da kujerunsu su ke rawa a dalilin barin jam’iyyar da ta ba su nasara a zabe.

Hukuncin Inyang Ekwo zai iya shafan gwamnonin jihar Zamfara, Kuros Riba da suka koma APC.

1. Ben Ayade

Gwamnan Kuros Riba, Ben Ayade da mataimakinsa Ivara Esu sun sauya-sheka daga PDP zuwa APC. ‘Yan siyasan sun yi watsi da PDP bayan sun zarce.

Kara karanta wannan

Karin bayani: PDP ta mika sunayen masu maye gurbin gwamnan APC da mataimakinsa da aka tsige ga INEC

2. Bello Matawalle

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle yana cikin wadanda suka canza jam’iyya. Sai dai wani Alkali ya yi fatali da karar da aka kai, yanzu za a je kotun koli.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daga baya an tsige mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Mahadi Aliyu Gusau wanda ya ki yarda ya sauya-sheka tare da gwamnan da wasu ‘yan majalisan jihar.

Gwamna Ayade
Ayade da manyan APC Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

‘Yan Majalisu

Akwai ‘yan majalisun dokokin jihar Edo da suka sauya-sheka zuwa jam’iyyar APC. Yanzu haka su na fuskantar barazana idan har jam’iyyar PDP ta kai su kotu.

3. Hon. Yekini Idaiye

‘Dan majalisa mai wakiltar mazabar Akoko-Edo 1 a majalisar dokokin jihar Edo ya koma APC a 2021.

4. Nosayaba Okunbor

‘Dan majalisa mai wakiltar mazabar Orhionmwon ta gabas a majalisar dokokin jihar Edo ya shiga APC.

Sanatoci

Akwai Sanatocin jihar Zamfara uku da suka sauya-sheka zuwa jam’iyyar PDP daga APC. Sai kuma masu wakiltar jihar Delta ta Arewa da Taraba ta Kudu.

Kara karanta wannan

Da Ɗuminsa: Kotu Ta Ƙwace Kujerun Ƴan Majalisa 16 Saboda Ficewa Daga PDP

5. Sahabi Ya’u

6. Lawali Hassan Anka

7. Mohammed Hassan

8. Peter Nwaoboshi

9. Emmanuel Bwacha

Rikicin PDP a Jigawa

A jihar Jigawa ana rigima a PDP tsakanin Mustafa Sule Lamido da Aminu Ibrahim Ringim wanda ya rike mukami a gwamnatin mahaifinsa watau Sule Lamido.

Shekaru takwas da saukar mahaifinsa daga kujerar Gwamna, wasu su na zuga Mustafa Lamido ya yi takarar Gwamna a 2023 bayan ya rasa takarar Sanata a 2019.

Asali: Legit.ng

Online view pixel