Tsige gwamnan Ebonyi: Shehu Sani ya bayyana abun da zai faru da sauran gwamnonin da suka sauya sheka

Tsige gwamnan Ebonyi: Shehu Sani ya bayyana abun da zai faru da sauran gwamnonin da suka sauya sheka

  • Sanata Shehu Sani ya magantu a kan hukuncin kotu da ta kori gwamnan Ebonyi, David Umahi daga kan kujerarsa
  • Sani ya bayyana cewa wannan hukunci zai shafi sauran gwamnoni masu ci da suka koma wata jam’iyyar
  • Babban kotun tarayya da ke Abuja dai ta kori Gwamna Umahi da mataimakinsa saboda sauya sheka daga PDP zuwa APC mai mulki

Tsohon sanata da ya wakilci yankin Kaduna ta tsakiya a majalisar dokokin tarayya ta takwas, Sanata Shehu Sani ya yi martani a kan hukuncin da kotu ta yankewa gwamnan jihar Ebonyi David Umahi.

A ranar Talata, 8 ga watan Maris, ne babban kotun tarayya da ke Abuja ta kori Gwamna Umahi da Mataimakinsa Dr Eric Kelechi Igwe, saboda sun fice daga jam'iyyar PDP zuwa APC.

Tsige gwamnan Ebonyi: Shehu Sani ya bayyana abun da zai faru da sauran gwamnonin da suka sauya sheka
Tsige gwamnan Ebonyi: Shehu Sani ya bayyana abun da zai faru da sauran gwamnonin da suka sauya sheka
Asali: UGC

Kotun, a hukuncin da Mai sharia Inyang Ekwo, ya yi, ta ce kuri'u 393,042 da Gwamna Umahi ya samu a zaben ranar 6 ga watan Maris na gwamnan Jihar Ebonyi, na jam'iyyar PDP ne kuma doka bata amince a mayarwa APC ba.

Kara karanta wannan

Karin bayani: PDP ta mika sunayen masu maye gurbin gwamnan APC da mataimakinsa da aka tsige ga INEC

A wani rubutu da ya yi a shafinsa na Twitter kan wannan hukunci, Sani, ya bayyana cewa hakan zai shafi sauran gwamnoni masu ci wadanda suka sauya sheka daga jam’iyyun da aka zabe su a karkashinsu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya rubuta a shafin nasa:

“Koran gwamnan Ebonyi da kotu ta yi zai shafi sauran gwamnoni masu ci wadanda suka sauya sheka.”

Kowawa APC: Gwamna Umahi Ya Yi Martani Kan Ƙwace Masa Ƙujera Da Kotu Ta Yi, Ya Bayyana Matakin Da Zai Ɗauka

A gefe guda, Gwamnan Jihar Ebonyi Dave Umahi ya ce zai daukaka kara bisa hukuncin da Babban Kotun Tarayya ta yanke a Abuja na kwace masa kujerarsa saboda komawa jam'iyyar APC, rahototon BBC Pidgin.

Yayin jawabin da gwamnan ya yi yayin taron manema labarai, gwamnan ya ce kotu bata da ikon cire shi daga ofishinsa.

Kara karanta wannan

‘Yan siyasa 9 da za su iya asarar kujerunsu a kotu a sakamakon sauya-sheka zuwa APC

Gwamna Dave Umahi da mataimakinsa Kelechi Igwe sun fice daga jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ne sun koma APC a shekarar 2020.

Bayan ficewarsu, wasu yan majalisar jihar da mataimakin gwamna suka fice daga PDPn suka bi sahun gwamnan zuwa APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel