Ana barazana ga rayuwata don na ki yarda a tsige mataimakin gwamna – Dan majalisar Zamfara

Ana barazana ga rayuwata don na ki yarda a tsige mataimakin gwamna – Dan majalisar Zamfara

  • Salihu Usman, mamba a majalisar dokokin jihar Zamfara ya koka kan cewa ana barazana ga rayuwarsa
  • Usman wanda ya kasance dan jam'iyyar PDP daya tilo a majalisar ya ce gwamnatin jihar na kokarin kama shi ta kulle don ya ki goyon bayan yunkurin tsige mataimakin gwamna
  • Sai dai gwamnatin Zamfara ta karyata hakan inda tace Gwamna Matawalle baya tsoma baki a harkokin da ya shafi majalisar jihar balle har ya yiwa wani mamba barazana

Zamfara - Dan majalisar dokokin jihar Zamfara, Salihu Usman, ya bayyana cewa ya gudu ya bar jihar saboda barazanar da gwamnatin jihar ke yi masa don ya ki goyon bayan yunkurin tsige mataimakin gwamna.

Mista Usman shine dan majalisa daya tilo da ya rage a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a majalisar bayan dukka sauran sun bi Gwamna Bello Matawalle zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a shekarar da ta gabata.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Hasalla Bayan Jami’an Tsaro Sun Kange Shi Daga Ganin Osinbajo a Yayinda Ya Ziyarci Jiharsa

Ana barazana ga rayuwata don na ki yarda a tsige mataimakin gwamna – Dan majalisar Zamfara
Ana barazana ga rayuwata don na ki yarda a tsige mataimakin gwamna – Dan majalisar Zamfara Hoto: BBC Hausa
Asali: UGC

Dan majalisar ya ki halartan zaman karshe da majalisar ta yi a makon da ya kamata wanda a lokacin ne yan majalisa 18 daga cikin 22 suka jefa kuri’un tsige mataimakin gwamnan jihar, Mahadi Ali.

Ana kallon duk wani motsina

Da yake zantawa da sashin Hausa na BBC a safiyar Litinin, 14 ga watan Fabrairu, dan majalisar ya ce jami’an gwamnatin jihar sun zuba mashi ido, mai yiwuwa don su kama shi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Usman ya ce:

“Ana kallon duk wani motsina. Na san kokari suke su kama ni saboda suna ganin zan kawo masu tarnaki a kokarinsu na tsige mai girma mataimakin gwamna. A yanzu, suna so su kama ni sannan su tsare ni saboda suna ganin zan iya hana kokarinsu a tsarin tsigewar.
“Koda dai ba a fada mani dalilin da yasa suke nema na ba, na tabbata gwamnatin jihar na son toshe bakina ne ta hanyar kama ni da kuma tsare ni. Ban san wasu tuhume-tuhume suke son suyi mun ba amma na san cewa rayuwata tana cikin hatsari. Na bar masu jihar yanzu.”

Kara karanta wannan

Gwamnatin Jigawa zata fara bawa masu juna biyu N5,000 a wata

Ya kara da cewa:

"Wannan daliline na kishin jam'iyyata ya sa na fara magana da 'yan majalisa 'yan uwana na nuna musu illar yarda ayi amfani da kai don musgunawa wani, domin duk abin da ka yi kai ma a gaba sai an yi maka.
"To shawarwarin da nake bayarwa ne ya sa har gwamnati ta ji su sannan ta fara bin diddigi don jin abin da nake cewa a Majalisar da ake gani kamar ina nema na ja ra'ayinsu."

Sai dai kuma sashin BBC ta kuma ruwaito cewa hadimin gwamnan Zamfara, Zailani Bappa ya karyata zargin domin a cewarsa Gwamna Bello Matawalle, ba ya katsalandan cikin harkokin Majalisar jihar.

Ya kuma ce babu ruwan gwamnan a cikin duk wani batu da ya shafi aikin majalisar, balle har ya yi wa wani dan majalisar barazana.

A raba ma kowa, zamu fara zaman tsige mataimakin gwamna: Kakakin Majalisar Zamfara

Kara karanta wannan

Sokoto: Kansila ya gwangwaje 'yan unguwarsa da kyautar tabarmai 2, ya jawo cece-kuce

A baya mun kawo cewa kakakin majalisar dokokin jihar Zamfara, Nasiru Magarya, ya umurci magatakardan majalisar, Shehu Anka, ya rabawa dukkan yan majalisa takardar fara shirin tsige mataimakin gwamna, Mahdi Gusau.

A cewar jawabin da mai magana da yawun majalisar, Mustafa Kaura, ya saki, ya bayyana cewa an yi hakan bisa sashe na 188 na kundin tsarin mulkin Najeriya.

Kaakin, a cewar jawabin, ya bayyana umurnin a zaman majalisan ranar Laraba domin baiwa sauran yan majalisa daman karanta laifukan da ake tuhuman mataimakin gwamnan da su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel