Gwamnatin Jigawa zata fara bawa masu juna biyu N5,000 a wata

Gwamnatin Jigawa zata fara bawa masu juna biyu N5,000 a wata

  • Gwamnatin Jigawa ta fito da ssabon tsarin biyan iyaye mata masu juna biyu kudin aljihu duba biyar a wata
  • Mataimakin Gwamnan jihar ya ce za'a fara biyan kudin ne ga mata 5000 daga karshen watan nan ta Febrairu
  • Gwamnatin jihar ta ce ta fito da tsarin ne domin taimakawa matan karkaka masu zuwa asibiti duba lafiyarsu

Dutse - Gwamnatin Jihar Jigawa ta bayyana cewa komai ya kankama don fara biyan mata masu juna biyu sama da mutum 5000 kudi dubu biyar-biyar a wata.

Mataimakain Gwamanan Jihar, Mallam Umar Namadi, ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da manema labarai a Dutse, babban birnin Jihar, rahoton Aminiya.

Namadi yace jihar ta bullo da shirin ne domin ya taimaka wa mazauna karkara don su rika zuwa awon ciki a asibiti kafin haihuwa.

Kara karanta wannan

2023: Gwamnan PDP dake son gaje Buhari ya shiga Katsina, ya jero matsalolin da za'a shiga idan APC ta zarce

Gwamnatin Jigawa zata fara masu juna biyu N5,000 a wata
Gwamnatin Jigawa zata fara masu juna biyu N5,000 a wata
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce gwamnatin Muhammad Badaru ta sanya wannan kudi cikin kasafin kudin 2022 da Gwamnan ya rattafa hannu.

Ya kara da cewa an bude wa kimanin mata 3,800 asusun ajiya na banki kuma za a fara biyansu a watan Fabrairun 2022,

Hakazalika suna kokarin yiwa sauran matan 1200.

An gurfanar da Saurayi gaban kotu kan yaƙi ɗaukar nauyin cikin da ya ɗirkawa budurwarsa

A wani labarin, kotun Majistire ta garƙame matashi ɗan shekara 24, Korode Yusuf, bisa ƙin ɗaukar ɗawainiyar cikin da ya ɗirkawa budurwarsa a jihar Ogun.

Premium Times ta rahoto cewa Yusuf, wanda ke zaune a No. 6 layin Kajola Oluwa, dake yankin Isale Ariya, na fuskantar tuhuma ne kan zargin jefa rayuwar wani cikin hatsari.

Mai gabatar da ƙara, E. O. Adaraloye, ya shaida wa kotu cewa, wanda ake ƙara ya aikata wannan ɗanyen aiki ne a ranar 1 ga watan Maris, 2021, a ɗakinsa da yake zaune.

Asali: Legit.ng

Online view pixel