Sokoto: Kansila ya gwangwaje 'yan unguwarsa da kyautar tabarmai 2, ya jawo cece-kuce

Sokoto: Kansila ya gwangwaje 'yan unguwarsa da kyautar tabarmai 2, ya jawo cece-kuce

  • ’Yan siyasar Najeriya dai sun yi fice wajen bayar da kyautuka na ban dariya ga al’ummar mazabunsu da sunan karfafa musu gwiwa
  • A jihar Sokoto ma wani kansila ya bi sahu, domin ya ba da wata kyautar banbarakwai ga wasu dattijai; kyautar tabarma
  • Ko da yake kansiloli, kamar dai yadda ‘yan majalisar jiha da na tarayya suke, akan zabe su ne domin samar da dokoki da gyara su

Kebbe, Sokoto - SaharaReporters ta wallafa wani rahoto da ke nuni da cewa wani kansila a jihar Sokoto ya baiwa al’ummar Sadada da ke karamar hukumar Kebbe da ke jihar tallafin tabarmai biyu na roba.

Kansilan, wanda ba a iya tantance sunansa ba, ya kuma dauki hotuna tare da wadanda suka amfana da kyautar a lokacin da yake mika tabarman garesu.

Kara karanta wannan

Gwamnoni da Majalisar Tarayya na neman taba karin albashin da aka yi ta bayan-fage

Kansila ya gwangwaje masoyansa da tabarmai
Sokoto: Kansila ya gwangwaje 'yan unguwarsa da kyautar tabarmai 2, ya jawo cece-kuce | Hoto: saharareporters.com
Asali: Twitter

Gudunmawar da kanslilan ya bayar ya haifar da cece-kuce a tsakanin ‘yan Najeriya, musamman 'yan Twitter.

Legit.ng ta bibiyi rahoton da SaharaReporters ta buga a shafin Twitter, inda muka tattaro muku kadan daga martanin jama'a.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kansila ya gamu da martanin 'yan Twitter

Elisha A. Olosunde ya rubuta cewa:

"Abin mamaki ba zai kare ba, maimakon ba da masana'antar tabarma, sun ba da gudummawar tabarma biyu kacal ga al'umma. Wace irin kasa muke ciki.”

Omotola Yekin Adedayo ya rubuta cewa:

"Wannan ba shi ne karon farko ba, na tuna wani lokaci ina kallon labaran NTA, inda aka ba da gudunmawar rediyo a yakin neman zabe a Arewa."

Jide Dina yace:

“Ku amince da labarai irin wannan, muna da sauran rina a kaba. Shin wannan romon dimokradiyya ne?..."

Jeffery Oseitua kuma yace:

"Wannan kasa ta gasu, amma jama'a ba su ma shirya don canji ba."

Kara karanta wannan

Ronaldo, Ozil, Mane da sauran ‘Yan kwallon kafa da suka fi kowa taimakawa marasa karfi

Omolagbon Samuel ya rubuta:

“Wannan wasa ne ko me? Nawa ne albashinsa a wata, kuma nawane kudin wadannan tabarman biyu? wannan wane irin wakili ne!!"

Kingsley Obida ya rubuta:

“Har yaushe ne wannan zai ci gaba a cikin kasa mai albarka da komai, amma duk da haka ‘yan kasar na rayuwa kamar matsiyata?
"Wacce daraja wadannan tabarman za su kara wa rayuwar wadannan mutanen da ke zaune a cikin wadannan al'ummomin da kuma yadda mutane za su yi amfani da su?"

Alheri danko: Wata kungiyar musulunci ta kawo alheri Kaduna, ta yi aikin jinyar ido kyauta

A wani labarin, Daily Trust ta rahoto cewa, wata kungiyar addinin musulunci mai suna Leen Charity Organisation ta zo da alheri, inda ta yi wa marasa galihu 100 maganin ido kyauta a jihar Kaduna.

Wanda ya kafa kungiyar ta Leen, Abdul’aziz Umar Abubakar, ya ce kungiyar tana kula da mutane ba tare da la’akari da addininsu ba.

Kara karanta wannan

Ya kamata PDP ta karɓe mulkin Najeriya, zaman lafiya ya gagara, inji gwamnan PDP

Ya ce kungiyar ta fahimci cewa mafi yawan masu fama da matsalar ido ba sa iya samun magani, lura da cewa masu fama da matsalar ido kamar hakiya ana tura su cibiyar kula da ido ta kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel