Gwamnan Arewa Ya Hasalla Bayan Jami’an Tsaro Sun Kange Shi Daga Ganin Osinbajo a Yayinda Ya Ziyarci Jiharsa

Gwamnan Arewa Ya Hasalla Bayan Jami’an Tsaro Sun Kange Shi Daga Ganin Osinbajo a Yayinda Ya Ziyarci Jiharsa

  • Gwamna Samuel Ortom na Jihar Binuwai ya bayyana yadda jami’an tsaro suka hana shi tarbar mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo
  • Ortom ya shaida yadda ya je har filin jirgin sama na rundunar sojin saman Najeriya da ke Makurdi a ranar Asabar duk din ya tarbi Osinbajo amma aka hana shi
  • Ya ce duk don nuna girmamawa ya saki duk ayyukan sa na jihar ya nufi filin jirgin wanda ya yi danasanin zuwa saboda tozarcin da ya fuskanta

Benue - Gwamna Samuel Ortom na Jihar Binuwai ya bayyana takaicin sa akan yadda jami’an tsaro suka hana shi shiga filin jirgin sama don tarbar mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, The Nation ta ruwaito.

Ortom ya ce ya je filin jirgin saman rundunar sojin Najeriya a ranar Asabar duk don tarbar mataimakin shugaba kasar wanda zai zarce Wukari a Jihar Taraba amma jami’an tsaro suka dakatar da shi.

Ortom Ya Hasalla Bayan Jami’an Tsaro Sun Kange Shi Daga Ganin Mataimakin Shugaban Kasa a Makurdi
Gwamnan Benue Ya Hasalla Bayan Jami’an Tsaro Sun Kange Shi Daga Ganin Osinbajo a Makurdi. Hoto: The Nation
Asali: UGC

Gwamna Ortom ya bayyana wa manema labarai a gidan gwamnati da ke Makurdi takarda daga fadar shugaban kasa wacce ta nuna cewa mataimakin shugaban kasar zai zarce Wukari daga Makurdi.

Saboda gudun yin laifi yasa ya je tarbarsa

Takardar wacce ta nuna kwanan watan 10 ga watan Fabrairun 2022, a jikin ta akwai sa hannun hadimin shugaban kasar Najeriya na musamman akan harkokin kasashen waje, Amb. Abdullahi Gwary, mai taken:

“Ziyarar da mai girma Farfesa Yemi Osinbajo, SAN GCON, mataimakin shugaban kasar Najeriya zuwa Wukari, Jihar Taraba, inda zai ya da zango ta NAF Base Makurdi, ranar Asabar, 12 ga watan Fabrairun 2022.”

Ortom ya ce duk don kada ya yi laifi, sai ya yanke shawarar ya bar wasu ayyukan jihar inda ya zarce filin jirgin don tarbar mataimakin shugaban kasar amma aka hana shi shiga.

A cewarsa ya fasa zuwa ta’aziyya ne don ya je tarbar mataimakin shugaban kasar

The Nation ta ruwaito yadda yace:

“Wani mummunan lamari ya auku yau wanda na yi matukar jin haushi akan yadda komai na kasar nan ya koma siyasa.
“Na so zuwa taron birniyar wani shugaban mu, Farfesa Ayua a Konshisha, amma sai na samu wata takarda wacce take nuna mataimakin shugaban kasa zai wuce Wukari daga Makurdi.
“Kamar yadda aka saba, idan shugaban kasa zai wuce ta jihar wani gwamna, gwamnan zai je ya tarbe shi. Don haka na tura mataimaki na don ya wakilce ni a birniyar Farfesa Ayua.
“Da safiyar nan da naje tarbar mataimakin shugaban kasar sai aka dakatar da ni a cikin jiha ta.”

Ortom ya ce idan aka ci gaba da mayar da komai siyasa, akwai matsala

Gwamnan ya ja kunne akan irin wannan abin inda ya ce in har hakan yana faruwa ci gaba zai tsaya.

Ya bayyana irin tsaka mai wuyar da jihar sa take ciki amma haka ya saki komai ya je tarbar mataimakin shugaban kasar, kuma hakan ya yi masa zafi kwarai.

Ya ce bai taba zagin shugaban kasa ko mataimakinsa ba amma akwai abubuwan da suke yi wadanda ba su da kyau.

Asali: Legit.ng

Online view pixel