A raba ma kowa, zamu fara zaman tsige mataimakin gwamna: Kakakin Majalisar Zamfara

A raba ma kowa, zamu fara zaman tsige mataimakin gwamna: Kakakin Majalisar Zamfara

  • Majalisar dokokin jihar Zamfara za ta fara zaman shirin tsige mataimakin gwamnan jihar Mahdi Aliyu Gusau
  • Majalisar na tuhumar mataimakin, wanda 'da ne ga tsohon Ministan tsaro, Janar Aliyu Gusau, da wasu laifuka
  • Mabiya sun dauke kafa daga ofishinsa tun bayan sanarwar majalisa na shirin tsigeshi

Gusau - Kakakin majalisar dokokin jihar Zamfara, Nasiru Magarya, ya umurci magatakardan majalisar, Shehu Anka, ya rabawa dukkan yan majalisa takardar fara shirin tsige mataimakin gwamna, Mahdi Gusau.

A cewar jawabin da mai magana da yawun majalisar, Mustafa Kaura, ya saki, ya bayyana cewa an yi hakan bisa sashe na 188 na kundin tsarin mulkin Najeriya.

Kaakin, a cewar jawabin, ya bayyana umurnin a zaman majalisan ranar Laraba domin baiwa sauran yan majalisa daman karanta laifukan da ake tuhuman mataimakin gwamnan da su.

Kara karanta wannan

Mataimakin Gwamnan Zamfara Ya Yi Babban Rashi, Matawalle Ya Yi Masa Ta’aziyya

Mataimakin gwamnaZamfara
A raba ma kowa, zamu fara zaman tsige mataimakin gwamna: Kakakin Majalisar Zamfara
Asali: Facebook

Mabiya sun dauke kafa daga ofishin mataimakin Gwamnan Zamfara

Mutane sun dauke kafa daga ofishin mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Barista Mahdi Aliyu Muhammad, biyo bayan shirin tsigeshi da majalisar dokokin jihar ke yi.

Daily Trust ta ruwaito tun bayan sauya shekan Gwamna Matawalle mataimakinsa Mahdi Gusau ya rage zuwa ofishinsa.

Majiyoyi sun bayyana cewa tuni mataimakin gwamnan ya daina zuwa ofis.

Majalisa ta lissafo laifukan Aliyu Gusau

Majalisar dokokin jihar Zamfara ta aikewa mataimakin gwamnan jihar Mahadi Ali takardar tsige shi.

Majalsar ta ce ana zargin mataimakin gwamnan ne da laifin yin amfani da mukaminsa, da wadata kansa da aikata laifuka ta hanyar amfani da kudaden jama'a da kuma gazawa wajen gudanar da ayyukan gwamnati.

Asali: Legit.ng

Online view pixel