2023: Kungiya ta bawa Osinbajo wa'adin kwanaki 30 ya fito ya nemi kujerar Buhari

2023: Kungiya ta bawa Osinbajo wa'adin kwanaki 30 ya fito ya nemi kujerar Buhari

  • Gabanin babban zaben shekarar 2023, wata kungiya mai goyon bayan APC ta nuna goyon bayanta ga Farfesa Yemi Osinbajo
  • Kungiyar ta kuma kara da cewa ta bawa mataimakin shugaban kasar wa'adin kwanaki 30 ya fito ya bayyana niyarsa na takarar shugaban kasa
  • A cewar kungiyar, an gwada kamun ludayin mataimakin shugaban kasar kuma an amince da shi, gashi ba shi da kabilanci don haka ya dace da aikin

FCT, Abuja - Kungiyar National Coalition Group, NCG, ta bawa Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo wa'adin kwana 30 ya bayyana niyarsa na fitowa takarar shugaban kasa a babban zaben 2023.

Kungiyar, a wasikar da ta aike wa mataimakin shugaban kasar a ranar Alhamis 27 ga watan Janairu da Legit.ng ta gani, ta ce sai gida ya koshi ake yi wa na waje tayi don haka shi APC ya dace ta tsayar a 2023.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: PDP ta shiga matsi, gwamnonin kudu 3 sun ce ba ruwansu da takarar Atiku

2023: Kungiya ta bawa Osinbajo wa'adin kwanaki 30 ya fito ya nemi kujerar Buhari
Kungiya ta bawa Osinbajo wa'adin kwanaki 30 ya fito ya nemi kujerar shugaban kasa a 2023. Hoto: Vanguard NG
Asali: Twitter

Wasikar da Fagbemi Opeyemi da Eli Eberechukwu Dibla, shugaba da sakataren kungiyar suka rattaba hannu a kai ta yi gargadin fuskantar babban zaben da dan takara sabon shiga.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani sashi na wasikar ya ce:

"2023 ne karo na farko da APC da yan Najeriya za su zabi sabon shugaba bayan jam'iyyar ta kammala wa'adin ta biyu a shekaru takwas.
"Kai ya kamata a fara yi wa tayi kuma zaben jin ra'ayi da muka yi a watanni shida da suka gabata ya nuna kaine dan takara mafi dacewa idan ana son samun nasara a 2023.
"Ba zai yi wu jam'iyyar mu ta tsayar da dan takara na gwaji ba a zaben 2023; Yan Najeriya sun yi magana ta zaben jin ra'ayin da muka yi, tsayar da kai shine zabi mafi kyau ga jam'iyyar domin 'yan Najeriya su shaki sabuwar iska.

Kara karanta wannan

Mu ba jam'iyyar siyasa bace: ACF ta gargadi mambobinta wajen marawa dan takara baya

"Mafi yawancin 'yan Najeriya, masu sarauta, kungiyoyin yan kasuwa, kungiyoyin dalibai, kungiyoyi masu zaman kansu fiye da 149 sun nuna cewa Osinbajo suke so a bawa tikitin APC a 2023."

Wasikar ta cigaba da cewa Osinbajo mutum ne haziki mai basira da tsoron Allah da girmama doka da oda kamar yadda aka gani a watannin da ya zama shugaban kasa na rikon kwarya.

Ta ce ana bukatar mutum mai gaskiya, haziki da zai dora a shugaban kasar idan Buhari ya kammala wa'adinsa a 2023, don haka ta roki Osinbajo ya fito takarar.

2023: Zan iya shugabancin Najeriya amma dai ban matsu ba, Orji Kalu

A wani labarin, bulaliyar Majalisar Dattawa, Orji Uzor Kalu, ya ce duk da a shirye ya ke da ya yi kamfen kuma zai iya shugabantar kasar nan, amma bai matse ya ce ai zama shugaban Najeriya ba, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ba gaskiya bane: Miyetti Allah ta yi watsi da batun goyon bayan Tinubu a zaben 2023

Kalu, tsohon gwamnan Jihar Abia, ya yi wannan bayanin ne a ranar Laraba yayin amsa tambayoyi daga manema labarai a Majalisar Tarayya, washegarin da ya kai wa Buhari ziyara a fadarsa da ke Abuja.

A cewarsa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, takarar shugaban kasa hukunci ne ‘yan Najeriya zasu yanke sannan ko wacce jam’iyya zata zabi bangaren da za ta bai wa damar tsayawa takara, musamman jam’iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel