2023: Zan iya shugabancin Najeriya amma dai ban matsu ba, Orji Kalu

2023: Zan iya shugabancin Najeriya amma dai ban matsu ba, Orji Kalu

  • Bulaliyar Majalisar Dattawa, Orji Uzor Kalu ya ce a shirye ya ke da ya yi kamfen din neman zaben shugabancin kasa amma bai nace lallai sai ya zama shugaban kasa ba
  • Kalu, tsohon gwamnan Jihar Abia a ranar Laraba ya furta hakan ne yayin amsa tambayoyin manema labarai a Majalisar Tarayya washegarin da ya kai wa Buhari ziyara a fadar sa
  • A cewarsa, takarar shugaban kasa hukunci ne wanda ‘yan Najeriya za su yanke da kuma tsarin karba-karbar da jam’iyyu suka shirya musamman APC

Bulaliyar Majalisar Dattawa, Orji Uzor Kalu, ya ce duk da a shirye ya ke da ya yi kamfen kuma zai iya shugabantar kasar nan, amma bai matse ya ce ai zama shugaban Najeriya ba, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2023: Ya zama tilas PDP ta samar da shugaban ƙasa a zabe mai zuwa, In Ji Fayose

Kalu, tsohon gwamnan Jihar Abia, ya yi wannan bayanin ne a ranar Laraba yayin amsa tambayoyi daga manema labarai a Majalisar Tarayya, washegarin da ya kai wa Buhari ziyara a fadarsa da ke Abuja.

2023: Zan iya shugabancin Najeriya amma dai ban matsu ba, Orji Kalu
Orji Kalu: Za iya shugabantar Najeriya amma ban matsu dole sai na zama shugaban kasar ba. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, takarar shugaban kasa hukunci ne ‘yan Najeriya zasu yanke sannan ko wacce jam’iyya zata zabi bangaren da za ta bai wa damar tsayawa takara, musamman jam’iyyar APC.

Kudu maso gabas a shirye take da ta tsayar da dan takara

A cewarsa, yankin kudu maso gabas a shirye take da ta samar da shugaban kasar da zai maye gurbin Buhari.

Kalu ya bayyana tattaunawar da suka yi da Buhari akan matsalolin da kasa take fuskanta, musamman batun tsaro, dokokin zabe da walwalar kasar nan.

Kara karanta wannan

Orji Kalu: Duk inyamurin da ya ayyana tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 bai san me yake ba

Yayin da aka tambaye shi idan ya sanar da burinsa na tsayawa takarar shugaban kasa, cewa ya yi:

“Na fadi cewa za a samar da shugaban kasa daga yankuna biyu da ke kasar nan. Ko dai yankin kudu maso gabas ko kuma arewa maso gabas. Dayan gurbin za a ba kudu maso gabas, kuma ina da damar da zan shugabanci kasa kuma zan iya. Zan iya zagewa in yi takara kuma in samu nasara.”

Ya ce idan lokaci ya yi zai fara kamfen

Kalu ya kara da cewa:

“Dan kabilar Ibo ba zai iya shugabancin kasa ba a takarar da za a sake. Na yarda yankin kudu maso gabas zasu iya kawo shugaban kasa na gaba kuma hakan zai faru.”

Kalu ya kara da cewa zai iya fara zagaye kasa don kamfen idan lokacin da ya dace ya yi.

2023: Wani gwamnan APC daga kudu ya nuna sha'awar gadon kujerar Buhari, ya bada sharaɗi

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Shugaban PDP ya yi magana kan magajin Buhari

A wani labarin, Gwamnan Jihar Cross River, Ben Ayade ya ce, zai fito takarar shugabancin kasa a shekarar 2023 idan jam'iyyarsa ta All Progressives Congress, APC, ta tsayar da shi.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 19 ga watan Janairu, a lokacin da aka yi hira da shi a wani shiri a Channels TV, The Cable ta ruwaito.

Da aka masa tambaya ko zai yi takarar shugabancin kasa a 2023 a karkashin inuwar jam'iyyar APC, gwamnan ya ce ya kamata jam'iyyarsa ta yi amfani da tsarin karba-karba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel