Ba gaskiya bane: Miyetti Allah ta yi watsi da batun goyon bayan Tinubu a zaben 2023

Ba gaskiya bane: Miyetti Allah ta yi watsi da batun goyon bayan Tinubu a zaben 2023

  • Kungiyar Miyetti Allah ta yi watsi da batun goyon bayan babban jagoran APC na kasa, Bola Tinubu a zaben 2023
  • A wani jawabi da ta saki, kungiyar ta ce babu gaskiya a rahotannin da ke yawo cewa bata tsayar da kowani dan takara da take muradin marawa baya ba
  • Ta ce wadanda suka ayyana goyon bayan Tinubu sun yi hakan ne don kansu amma ba da yawun kungiyar ba

Abuja - Kungiyar Miyatti Allah ta Najeriya (MACBAN), ta ce bata goyon bayan kudirin takarar shugabancin kowani dan takara a babban zaben 2023.

Babban sakataren MACBAN, Alhaji Baba Ngelzarma, ya bayyana hakan a wata sanarwa ga manema labarai a ranar Laraba, 25 ga watan Janairu, a Abuja, PM News ta rahoto.

Ba gaskiya bane: Miyetti Allah ta yi watsi da batun goyon bayan Tinubu a zaben 2023
Ba gaskiya bane: Miyetti Allah ta yi watsi da batun goyon bayan Tinubu a zaben 2023 Hoto: PM News
Asali: Twitter

Ngelzarma ya ce kungiyar tana mutunta takarar dukkanin yan takarar shugaban kasa sannan cewa lokaci bai yi da za ta fitar da wanda zata marawa baya ba, rahoton Daily Post.

Kara karanta wannan

2023: Ƙungiyar kare hakkin musulmi ta caccaki Afenifere kan goyon bayan Tinubu

Ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“An ja hankalin hedkwatar kungiyar MACBAN na kasa zuwa ga labarai a kafofin watsa labarai da ke ikirarin cewa mun marawa takarar shugabancin Sanata Ahmed Tinubu baya.
“Muna so mu yi karin haske cewa kungiyar bata marawa kowani dan takara baya ba.
“Wadanda suka marawa Tinubu baya suna haka ne a matsayinsu na mutane masu zaman kansu, don haka kada a jefa MACBAN cikin siyasar lamuncewa wani a wannan matakin.”

Babban jagoran jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Tinubu, a ranar Litinin, 10 ga watan Janairu, ya sanar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari aniyarsa ta tsayawa takara a zaben 2023.

Tinubu, wanda ya yi magana bayan wata ganawar sirri da Buhari a fadar shugaban kasa, Abuja, ya ce koda dai ya ayyana aniyarsa ga Shugaban kasar, zai ci gaba da tuntubar yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Shugaba a 2023: Fulani sun yi watsi da 'yan takara daga Arewa, sun fadi zabinsu

Shugaba a 2023: Fulani sun yi watsi da 'yan takara daga Arewa, sun fadi zabinsu

A gefe guda, mun ji cewa, wata Kungiya mai suna Fulani Political Forum, ta shiga jerin magoya bayan jagoran jam’iyyar APC, Bola Tinubu a yakin neman tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.

Shugaban kungiyar, Alhaji Ya’u Haruna, ya bayyana goyon bayansu ga Tinubu a wani taron kasa da ya samu halartar shugabannin NPF daga sassan kasar a Abuja.

Alhaji Ya’u, wanda tsohon mataimakin shugaban kungiyar Miyetti Allah Kautal-Hure (Arewa maso Yamma) ne na kasa, ya bayyana cewa kungiyar ta amince da Tinubu ne saboda damuwarsa kan halin da Fulani ke ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel