Mu ba jam'iyyar siyasa bace: ACF ta gargadi mambobinta wajen marawa dan takara baya

Mu ba jam'iyyar siyasa bace: ACF ta gargadi mambobinta wajen marawa dan takara baya

  • Kungiyar ACF ta gargadi mambobinta a kan lamuncewa yan takarar da ke neman kujerar shugabancin kasa a zaben 2023 mai zuwa baya
  • Shugaban kungiyar, Audu Ogbeh, ya bayyana cewa kungiyar ba jam'iyyar siyasa bace don haka babu ruwanta da batun tsayar da dan takara
  • Ogbeh ya ce basa sanya baki a harkokin siyasar kasar sai dai idan yin hakan ya zama tilas kamar yadda suke kokarin zama da kungiyoyin kudu don wanzar da zaman lafiya

Kaduna - Kungiyar tuntuba ta arewa (ACF) ta gargadi mambobinta a kan goyawa yan takarar da ke neman kujerar shugabancin kasa a zabe mai zuwa baya.

Shugaban kungiyar kuma tsohon ministan noma, Audu Ogbeh, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba, 27 ga watan Janairu a jawabinsa na bude taro a taron kungiyar NEC a Kaduna, The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Zan kawar da karuwai idan nayi nasara a zabe, Dan takaran shugaban kasa yayi alkawari

Ya ce ACF ba jam'iyyar siyasa bace, don haka, ba za ta iya lamuncewa kowani dan takarar shugaban kasa ba.

Mu ba jam'iyyar siyasa bace: ACF ta gargadi mambobinta wajen marawa dan takara baya
Mu ba jam'iyyar siyasa bace: ACF ta gargadi mambobinta wajen marawa dan takara baya Hoto: Vanguard
Asali: Facebook

Ogbeh ya kuma ce ACF na shirye-shiryen ganawa da kungoyi a kudu maso gabas, kudu maso yamma da kudu maso kudu a kokarinta na habbaka wanzuwar zaman lafiya a tsakanin yan Najeriya gabannin babban zabe mai zuwa, rahoton Channels TV.

Ogbeh ya ce:

"Tsare-tsarenmu na ganawa da kungiyoyin Afenifere, Ohanaeze, south-south people congress yana nan kan hanya saboda akwai bukatar dakatar da kalaman batanci a kan yankunan kasar.
"Ya kamata mu janye daga goyon bayan kowani dan takara don zaben shugaban kasa na 2023. Idan kowa ya tambaye ka game da goyon baya, ka fada ma wannan cewa mu ba jam'iyyar siyasa bane.

Kara karanta wannan

Ba gaskiya bane: Miyetti Allah ta yi watsi da batun goyon bayan Tinubu a zaben 2023

"Har ga 2023, ba mu riga mun san wanene dan takarar ba. Mu ba jam'iyyar siyasa bane. Ba ma shiga harkokin siyasa sai dai a inda ya zama dole.
"Allah ya taimake mu da yan takara nagari. Allah kadai ne zai iya magance matsalarmu.
"Akwai bukatar mu wanzar da zaman lafiya. Kalaman batanci a kafofin sadarwa ba zai taimake mu ba. Bama son rikici a wannan kasar. Idan muka zama marasa galihu, ina za mu je? Za mu bar dukka dukiyoyinmu saboda ba za mu iya daukar komai-da-komai ba baya ga jakunkunan Ghana-must-go."

Shugaban na ACF ya kuma nuna damuwa kan rahotannin ayyukan kungiyoyin asiri a makarantu sannan ya yi kira ga gwamnati a dukkan matakai da su tabbatar da kare yaran makaranta.

Dan majalisa daga Gombe ya lissafo gwanayensa, ya ce daya daga cikinsu ne ya cancanci ya gaji Buhari

A wani labarin, dan majalisar wakilai mai wakiltan mazabar Kaltungo/Shongom na Gombe, Hon Simon Karu, ya bayyana yan takarar da suka cancanci su gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Shugaba a 2023: Fulani sun yi watsi da 'yan takara daga Arewa, sun fadi zabinsu

A cewar Karu, mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Raji Fashola ko Femi Gbajabiamiala ne suka cancanci samun tikitin takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

A wata hira da aka yi da shi, dan majalisar ya ce kowanne daga cikinsu zai kai kasar ga matakin ci gaba idan har aka mika mulki ga yankin kudu, The New Telegraph ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel