PDP Ta Nemi Buhari Ya Shiga Tsakanin Gwamnan APC Da Tsohon Ɗan Majalisar Tarayya

PDP Ta Nemi Buhari Ya Shiga Tsakanin Gwamnan APC Da Tsohon Ɗan Majalisar Tarayya

  • Babban Jam'iyyar hamayya a Najeriya ta PDP reshen Jihar Ebonyi ta yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya saka baki a rikicin da ya taso a jihar
  • A baya-bayan nan dai Gwamna Dave Umahi na Ebonyi ya ayyana neman tsohon dan majalisar tarayya kuma jigo a PDP, Linus Okorie, ruwa a jallo kan wallafar da ya yi a Facebook
  • Gwamnatin na Ebonyi ta yi ikirarin cewa rubutun da Okorie ya wallafa sun taimaka wurin tunzura mutane suka hallaka wani jami'in tsaro na Ebubeagu
  • Amma PDP din ta ce gwamnatin Jihar bita da kulli kawai ta ke yi wa Okorie kana ta ce gwamnatin jihar ba ta da ikon ayyana neman wani ruwa a jallo

Jihar Ebonyi - Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta bukaci Shugaba Muhammadu Buhari ya saka baki a kan rikicin da ke faruwa a jihar, The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Matsayin Da Ake Ciki Akan Sulhu da yan tsagin Gwamna Ganduje, Malam Ibrahim Shekarau

A ranar Talata, gwamnatin Jihar Ebonyi ta ayyana neman Linus Okorie, tsohon dan majalisa, wanda kuma dan jam'iyyar PDP ne ruwa a jallo, kan zarginsa da wallafa rabutu masu tunzura mutane a Facebook.

PDP Ta Nemi Buhari Ya Shiga Tsakanin Gwamnan APC Da Tsohon Ɗan Majalisar Tarayya
PDP Ta Nemi Buhari Ya Shiga Tsakanin Gwamnan Ebonyi Da Tsohon Ɗan Majalisar Tarayya. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Uchenna Orji, kwamishinan labarai na Jihar, ya yi ikirarin cewa rubutu mai tunzura mutane da tsohon dan majalisar ya wallafa a Facebook yana da alaka da kisar gillar da aka yi wa jami'in tsaro na Ebube Agu.

Amma tsohon dan majalisan ya musanta hakan, yana mai cewa Umahi kawai yana neman wani babban mutum da zai yi misali da shi ne don kawar da hankalin mutane game da rasa rayyukan jami'an Ebube Agu a jihar.

Muna kira da Buhari, Majalisar Tarayya da kasashen waje su ceto demokradiyya, Okorie

Kara karanta wannan

Kakakin PDP ya gurfana a gaban kotu kan caccakar gwamnan APC a Facebook

Da ya ke martani kan ayyanawar a ranar Laraba, Tochukwu Okorie, shugaban PDP na Ebonyi, ya ce gwamnan ba shi da ikon ayyana neman tsohon dan majalisar ruwa a jallo.

Jaridar ta ruwaito ya ce:

"Gwamnan, a wani mataki na amfani da ikonsa ba yadda ta dace ba tare da saba wa kundin tsarin mulki, ya ayyana neman Linus Okorie, jigo a jam'iyyar mu, ruwa a jallo.
"Wannan alama ce da nuna hatsarin da Ebonyi da mutanen Ebonyi ke fuskanta; kundin tsarin mulki da dokar Najeriya ya nuna karara yadda ake yin hakan.
"Babu inda a dokan Najeriya ko wani wuri da gwamnatin jiha ko jami'anta ke da ikon aikata hakan.
"Muna kira ga shugaban kasa, majalisar tarayya da kasashen ketare su saka baki su dakatar da yiwuwar rushewar dokokin demokradiyya a Ebonyi."

2023: Tsohon hadimin Atiku ya 'soki' Saraki da Tambuwal kan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta amince a bada kwangilolin wasu tituna 16 da za su ci Naira Biliyan 64

A wani labarin, Jigo a jam’iyyar PDP a Jihar Ogun, Segun Showunmi a ranar Juma’a ya kalubalanci tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Dr Bukola Saraki da gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Tambuwal akan tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Daily Trust ta ruwaito.

A cewar Showunmi wanda tsohon kakakin dan takarar jam’iyyar PDP a zaben shekarar 2019, Atiku Abubakar ne, Tambuwal da Saraki ba sa da gogewar da za su iya mulkar cukurkudaddiyar kasa kamar Najeriya.

Ya tsaya akan cewa Atiku ne kadai wanda ya fi dacewa ya tsaya takarar a PDP kuma ya lashe zaben 2023 da ke karatowa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel