2023: Tsohon hadimin Atiku ya 'soki' Saraki da Tambuwal kan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP

2023: Tsohon hadimin Atiku ya 'soki' Saraki da Tambuwal kan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP

  • Wani jigo na jam’iyyar PDP a Jihar Ogun, Segun Showunmi ya kalubalanci tsohon shugaban majalisar dattawa, Dr Bukola Saraki da gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Tambuwal akan tsayawa takarar shugaban kasa
  • Kamar yadda ya ce a ranar Juma’a, Daga Tambuwal har Saraki babu mai gogewar da zai iya tsayawa tsayin-daki wurin mulkar kasa mai al'umma daban-daban kamar Najeriya
  • A cewarsa Atiku shi ne dan takarar da ya fi dacewa ya tsaya a karkashin jam’iyyar PDP don ya samu nasarar lashe zaben 2023 da ya ke karatowa

Ogun - Jigo a jam’iyyar PDP a Jihar Ogun, Segun Showunmi a ranar Juma’a ya kalubalanci tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Dr Bukola Saraki da gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Tambuwal akan tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gargadin wasu ga PDP: Kada ku ba 'yan shekara 70 tikitin takarar shugaban kasa a 2023

A cewar Showunmi wanda tsohon kakakin dan takarar jam’iyyar PDP a zaben shekarar 2019, Atiku Abubakar ne, Tambuwal da Saraki ba sa da gogewar da za su iya mulkar cukurkudaddiyar kasa kamar Najeriya.

2023: Tsohon hadimin Atiku ya 'soki' Saraki da Tambuwal kan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP
2023: Har yanzu da sauran ku, hadimin Atiku ya kallubalanci takarar Tambuwal da Saraki na kujeran shugaban kasa a PDP. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Atiku ne ya fi dacewa da mulkin Najeriya

Ya tsaya akan cewa Atiku ne kadai wanda ya fi dacewa ya tsaya takarar a PDP kuma ya lashe zaben 2023 da ke karatowa.

Showunmi ya yi wannan furucin ne ta wata takarda wacce ya bai wa manema labarai a Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun a matsayin martani ga kakakin kungiyar PDP Action 2023, Dr Rufus Omeire.

Dama a baya Daily Trust ta ruwaito yadda Dr Omeire ya kada baki ya ce Atiku ba ya da salo da dabarun da zai iya sarrafa Najeriya ko kuma gogewar da zai darewa mulkin Najeriya.

Kara karanta wannan

Magance tsaro: Tinubu ya bada tallafin miliyoyin Nairori ga jihar Neja

Omeire ya kira Atiku da dan kore ga tsohon shugaban lokacin ya yi mataimaki, Olusegun Obasanjo, wanda bai taba rike wani mukami ba idan aka hada shi da Saraki da Tambuwal da suka rike kujerar gwamna, ‘yan majalisu da sauran su.

Sai dai a bangaren Showunmu ya ce dukan su ba su kai gefen Atiku ba wurin iya aiki, jajircewa, gogewa da kuma dakakkiyar zuciyar da ake bukatar a samu wurin wanda zai gaji Buhari ba.

Ya ce dukan su ‘yan koyo ne a gafen Atiku

Kamar yadda ya ce:

“Yadda ake kwatanta su da Atiku ya yi matukar bani mamaki. A tambaye su idan sun taba yin gogayya a ofisoshin gwamnati kamar shi a ji.
“Idan ka kalli yadda suka kasa a mukaman da suka rike na ofishoshin da suka yi aiki sai ka sha mamaki. Saboda tsabar rashin gogewar su, ba kamar Atiku ba wanda ya yi aiki da hukumar kwastam kuma ya zama mataimakin shugaban kasa ba.

Kara karanta wannan

2023: Zan iya shugabancin Najeriya amma dai ban matsu ba, Orji Kalu

“Ko a jihohin su da suke gwamnoni babu abinda suka tsinana idan ka hada su da saura jihohin da aka kafa su a can bayan su.”

Ya kara da cewa babu yadda za a yi na Sokoto (Tambuwal) ya hada kansa da wanda ya rike mukamin mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.

A cewarsa kawai suna son su nuna wa duniya cewa sun kawo karfi ne kuma idan aka hada gogewar Atiku da su, za su zama kamar ‘yan koyo ne.

2023: Zan iya shugabancin Najeriya amma dai ban matsu ba, Orji Kalu

A wani labarin, bulaliyar Majalisar Dattawa, Orji Uzor Kalu, ya ce duk da a shirye ya ke da ya yi kamfen kuma zai iya shugabantar kasar nan, amma bai matse ya ce ai zama shugaban Najeriya ba, Daily Trust ta ruwaito.

Kalu, tsohon gwamnan Jihar Abia, ya yi wannan bayanin ne a ranar Laraba yayin amsa tambayoyi daga manema labarai a Majalisar Tarayya, washegarin da ya kai wa Buhari ziyara a fadarsa da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Na raba wa mutane Naira miliyan 140 jajibarin zaɓen 2003 duk da na san ba zan yi nasara ba, Olusegun Osoba

A cewarsa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, takarar shugaban kasa hukunci ne ‘yan Najeriya zasu yanke sannan ko wacce jam’iyya zata zabi bangaren da za ta bai wa damar tsayawa takara, musamman jam’iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel