Matsayin Da Ake Ciki Akan Sulhu da yan tsagin Gwamna Ganduje, Malam Ibrahim Shekarau

Matsayin Da Ake Ciki Akan Sulhu da yan tsagin Gwamna Ganduje, Malam Ibrahim Shekarau

  • Jagoran yan majalisar dokokin da suka raba jam'iyyar APC gida biyu ya bayyana inda aka kwana kan sulhu
  • Yayinda ake shirin taron gangamin APC a Febrairu, uwar jam'iyya na kokarin dinke barakar dake jihar Kano
  • Tsagin Malam Shekarau sun samu nasara a kotun tarayya dake birnin tarayya Abuja

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma Sanata mai wakiltan Kano ta tsakiya a majalisar datttawa, Malam Ibrahim Shekarau, ya yi tsokaci kan zaman sulhu da ke gudana tsakaninsu da bangaren Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Za ku tuna cewa a ranar Talata, 25 ga watan Junairu, 2022, tsagin jam'iyyun APC biyu sun hadu a zaman sulhun da Shugaban jam'iyyar APC, Mai Mala Buni ya shirya.

Shekarau a jawabin da ya saki ranar Alhamis ya bayyana cewa babban burinsu shi ne a tabbatar da tsarin gaskiya da adalci wajen samar da shugabanci a jam’iyyar APC a dukkan matakai ta hanyar mutuntawa, da girmamawa.

Kara karanta wannan

Da duminsa:Tsohon shugaban majalisar dattawa ya kuduri aniyar gaje kujerar Buhari

Malam Ibrahim Shekarau
Matsayin Da Ake Ciki Akan Sulhu da yan tsagin Gwamna Ganduje, Malam Ibrahim Shekara Hoto: Ibrahim Shekarau
Asali: Facebook

Malam Shekarau yace:

"A bisa wannan yunkuri na jam’iyya da shugabanni na kasa, na samar da masalaha da samar da mafita a cikin wannan jayayya na jam’iyya a jahar Kano, shugabannin jam’iyya bisa jagorancin shugaban jam’iyya na kasa Mai Girma Gwamnan Jahar Yobe, suka nemi mu don tattaunawa akan halin da ake ciki, wannan gayyata ita ce ta haifar da haduwarmu tare da shugabanni na kasa da kuma wakilan Mai Girma Gwamnan Jahar Kano, wadda aka yi a ranar Talata 25 ga watan January, wannan tattaunawa ba ta yanke wani hukunci ba, ba a yanke wata matsaya ba.
Mun tashi akan cewa za a ci gaba da tattaunawa bisa jagorancin shugaban jam’iyya, don haka muna tabbatarwa da al'umma cewar za mu ci gaba da sanar da su halin da ake ciki

Kara karanta wannan

Fadar Shugaban kasa ta tonawa Gwamnan PDP asiri, ta ce ya fi kowa rashin biyan albashi

Kuma muna tabbatarwa al'umma cewar za mu tsare mutuncin ‘yan jam’iyyar APC akan kowane mataki tare da tabbatar da sharuda wanda za su tabbatar da adalci ga dukkannin ‘yan jam’iyya da kuma al'ummar jahar Kano."

Tsagin shekarau ya sake yin nasara kan tsagin Ganduje a kotu

A ranar 13 ga Junairu, wata babbar kotun birnin tarayya da ke Abuja ta ki amincewa da bukatar da wasu ‘yan jam’iyyar APC na jihar Kano da ke biyayya ga gwamna Ganduje suka nema na yin watsi da hukuncin da ya tabbatar da zabukan jam’iyyar a taron gangaminta da aka yi.

Kotun da ke zama a karkashin Mai shari’a Hamza Muazu ta kuma ki amincewa da batun da aka shigar na dakatar da aiwatar da hukuncin har sai an yanke hukuncin daukaka kara a kotun daukaka kara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel