Gwamnatin Buhari ta amince a bada kwangilolin wasu tituna 16 da za su ci Naira Biliyan 64

Gwamnatin Buhari ta amince a bada kwangilolin wasu tituna 16 da za su ci Naira Biliyan 64

  • A ranar Laraba, 26 ga watan Junairu 2022, majalisar zartarwa ta kasa tayi taron da ta saba duk mako
  • Majalisar FEC ta amince a kashe N64,686,536,230 a kan wasu ayyukan tituna da za ayi a kasar nan
  • Isa Pantami, Bello da Garba Shehu sun yi bayani bayan an fito taron a fadar shugaban kasa a Abuja

Abuja - Kamar yadda This Day ta fitar da rahoto, a karshen taron FEC da aka yi jiya, an amince da kwangilolin hanya na N64,686,536,230 da za a yi a Najeriya.

Majalisar ta kuma amince a fara amfani da manhajar Revenue Assurance Solution (RAS) domin ya taimakawa hukumar NCC wajen rage facaka da dukiyar kasa.

Ministan birnin tarayya, Mohammed Bello da takwaransa na harkar sadarwa, Ali Isa Pantami da Garba Shehu sun yi magana da ‘yan jarida bayan taron na jiya.

Kara karanta wannan

Kotu ta zabi ranar Valentine don yanke wa Hushpuppi hukunci a Amurka

Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya ce an amince da ayyukan gadoji da tituna da ma’aikatar ayyuka za tayi a duk yankin kasar nan.

Fashola ya samu kwangiloli 15

Ma’aikatar ayyuka da gidaje na tarayya ta bukaci damar gina tituna da gadoji 15, kuma an amince.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnatin Buhari
Ana taron FEC a Aso Villa Hoto: www.thisdaylive.com
Asali: UGC

Garba Shehu ya ce daga cikin hanyoyin akwai na fadada titin Ikot-Ekpene-Aba zuwa Owerri wanda zai ci N40,157,000,000, za a dauki watanni 30 ana aikin.

Daily Trust ta rahoto hadimin shugaban kasar yana cewa za a gina wani titi a garin Offa, jihar Kwara. Wannan aiki na tsawon shekara daya zai ci N4,335,000,000.

Akwai kuma gyaran hanyar Alesi-Ugep a jihar Kuros Riba. An kara kudin wannan kwangila daga N11.221b zuwa N14.74b ana sa ran za a karasa cikin watanni shida.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun kama mutane 28, sun kwato makamai da layoyi a jihar Neja

Ministan birnin tarayya, Malam Mohammed Bello ya ce an amince da wani aikin titi na N5.454b da zai taimaka wajen rage cinkoson da ake yawan samu a garin Abuja.

Ana sa ran a kammala aikin titin Mpape zuwa Galuyi har Shere a Bwari. Kamfanin Vipan Global Investment Limited aka ba wannan kwangila da zai ci watanni 18.

Zaben 2023

An ji cewa shugaban kungiyar Vanguard for Justice ya ja-kunnen PDP, ya ce idan aka hana yankin Kudu kawo 'dan takarar shugaban kasa, PDP za ta zama tarihi.

Emmanuel Nduka ya ce idan ana neman adalci da zaman lafiya, dole Arewa su hakura da mulki da zarar Muhammadu Buhari ya gama wa’adinsa na shekaru takwas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel