Kakakin PDP ya gurfana a gaban kotu kan caccakar gwamnan APC a Facebook

Kakakin PDP ya gurfana a gaban kotu kan caccakar gwamnan APC a Facebook

  • An gurfanar da kakakin jam'iyyar PDP, Chika Nwoba, na jihar Ebonyi a gaban wata kotun majistare kan zargin sa da wallafa labaran karya
  • A wallafar Nwoba a shafin sa na Facebook, Gwamna Dave Umahi ya zarge sa da rubuta labaran karya wadanda za su iya hargitsa jihar
  • Bayan mika shi gaban kotu, alkalin ta aike shi gidan yari, lamarin da lauyan sa ya ce zai bibiya domin a fitar da wanda ya ke karewa

Ebonyi - An gurfanar da kakakin jam'iyyar PDP na Jihar Ebonyi, Chika Nwoba, a kotun majistare a Abakaliki bisa zargin sa da wallafa labaran karya kan Gwamna Dave Umahi.

An zarge shi da wallafa labarin kanzon kurege a shafin sa na Facebook akan Gwamna Dave Umahi wanda mai gurfanarwan yace zai iya kawo tangarda ga zaman lafiyan al'umma, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Zamfara: An gurfanar da dillalin motocci kan zargin cin 'sassan jikin yaro' ɗan shekara 9

Kakakin PDP ya gurfana a gaban kotu kan caccakar gwamnan APC a Facebook
Kakakin PDP ya gurfana a gaban kotu kan caccakar gwamnan APC a Facebook. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC

Kamar yadda ake tuhumar sa da laifuka 15, abun hukuntawa ne karkashin sashi na 4 na haramcin cin zarafi a kafar sada zumunci a dokar shari'a mai lamba 012 ta shekarar 2021.

Ebubeagu Security Network ta cafki Nwoba kusan sati uku da suka gabata yayin da ta mika sa ga 'yan sanda dan gurfanarwa wanda ya tunzurar da jam'iyyar sa.

An gurfanar da shi ne wasu kwanaki da suka gabata, sai dai ya yanke jiki ya fadi a kotun, inda aka mikasa zuwa ga asibiti kamar yadda kotu tayi umarni.

Premium Times ta ruwaito cewa, Duk da Nwoba ya musanta tuhumar da ake masa, kotun wacce ta ke karkashin alkalancin Blessing Chukwu, ta ce bata da hurumin karbar wannan karar.

Ta yi umarni da 'yan sanda su cigaba da tsare Nwoba har a yi masa gwajin korona kafin a kai sa gidan yari inda daga nan aka dage shari'ar zuwa 4 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Neman adalci: Makashin Hanifa ya bayyana a kotu, an dage shari'a zuwa wasu kwanaki

Lauyan Nwoba, Luke Nkwegu, ya karyata wallafar cin zarafin a kafar sada zumuntar da ake tuhumar wanda yake karewa.

Ya roki kotu da ta bayar da belin wanda yake karewan, inda a farfajiyar kotun lauyan ya bayyanawa manema labarai cewa zai yi kokari ya ga ya fidda Nwoba.

Zamfara APC: Rikici ya dauka sabon salo, ana amfani da 'yan daba wurin kai farmaki

A wani labari na daban, rikicin cikin gida na cigaba da rincabewa a jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta jihar Zamfara inda sabon salo ya kunno kai a cikin tsagi daban-daban na jam'iyyar ta yadda ake daukar nauyin kai farmaki da 'yan daba.

Daily Trust ta ruwaito cewa, tsagin tsohon gwamna Abdulaziz Yari ya nuna firgici da tashin hankali a jihar inda suke zargin za a mayar da jam'iyyar filin daga inda 'yan daba ke baje-kolin su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel