Yanzu-Yanzu: Majalisa ta sake yin sabon garambawul ga dokar zaɓe

Yanzu-Yanzu: Majalisa ta sake yin sabon garambawul ga dokar zaɓe

  • Majalisun tarraya na Dattawa da Wakilai sun yi tarayya wurin yi wa dokar zabe ta Najeriya garambawul gabanin babban zaben 2023
  • Majalisun biyu sun amince kan sashi na 84 inda ya bawa jam'iyyun siyasa damar tsayar da 'yan takara ta hanyoyi uku da suka hada da 'yar tinke, wakilai da sasanci
  • Da farko majalisar ta dage kan cewa yar tinke kadai jam'iyyun za su iya amfani da shi hakan yasa Shugaba Buhari ya ki saka hannu kan dokar zaben

FCT, Abuja - A wani gajeran zama ta da ta yi a ranar Talata, Majalisar Dattawar Najeriya ta sake yin wani garambawul ga dokar zabe ta kasa, Premium Times ta ruwaito.

Yan majalisar sun yi gyara ne a sakin layi na 84 na kudirin dokar ta zabe da aka dade ana cece-kuce a kansa.

Kara karanta wannan

Na gwammaci yashe teku: Cece-kuce yayin da budurwa ta rokon saurayi ya aureta

Sakin layin yana magana ne kan irin tsarin da jam'iyyun siyasa za su yi amfani da shi domin zaben yan takararsu.

Yanzu-Yanzu: Majalisa ta sake yin sabon garambawul ga dokar zaɓe
Majalisa ta sake yin sabon garambawul ga dokar zaɓe. Hoto: Premium Times
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da farko, Majalisar a 2021, ta umurci cewa tsarin 'yar tinke ne kawai jam'iyyun siyasan za su iya amfani da shi wurin zaben yan takararsu.

Dalilin da yasa Buhari ya ki saka hannu kan dokar zaben

Amma Shugaba Muhammadu Buhari ya ke amincewa da hakan ya bada dalili na rashin tsaro, tsadar yin zaben cikin gida da dakile damar yan Najeriya na shiga a dama da su a gwamnati.

Ya yi alkawarin zai saka hannu kan dokar idan an yi garambawul a sashin don a kara tsarin zabe ta hanyar wakilai wurin fitar da yan takarar jam'iyya.

A makon da ta gabata, Majalisar Dattawa da Wakilai duk sun yi wa dokar garambawul.

Kara karanta wannan

2023: Miyetti Allah ta ce ta na bayan Tinubu, ta bayyana taimakon da ya yi mata a baya

A yayin da Majalisar Dattawa ta bada zabin yar tinke, wakilai da sasanci wurin fitar da 'yan takara, Majalisar Wakilai kawai ta amince da yar tinke ne da tsarin wakilai.

Amma daga bisani, majalisun biyu sun sake garambawul don amincewa da tsarin guda uku a matsayin hanyoyin da jam'iyyun siyasa za su iya amfani da su don fitar da 'yan takara.

2023: Za mu bi didigin inda ƴan takara suke samo kuɗi, za mu sa ido kan asusun bankin ƴan siyasa, INEC

A wani rahoton kun ji cewa Hukumar zabe mai zaman kanta na Najeriya, INEC, ta aika da muhimmin sako ga yan siyasa da jam'iyyun siyasa gabanin babban zaben shekarar 2023.

Hukumar ta sha alwashin cewa za ta saka idanu a kan 'yan siyasa da jam'iyyun siyasa domin gano inda suke samo kudade domin yakin neman zabe, Vanguard ta ruwaito.

Shugaban INEC na kasa, Farfesa Mahmood Yakubu, wanda ya bayyana hakan yayin wani taro da hukumar zaben ta shirya a Abuja, ranar Juma'a 21 ga watan Janairu, kuma ya ce hukumar za ta saka ido kan yadda aka hada-hadar kudade ranar zabe don dakile siyan kuri'u, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel