2023: Miyetti Allah ta ce ta na bayan Tinubu, ta bayyana taimakon da ya yi mata a baya

2023: Miyetti Allah ta ce ta na bayan Tinubu, ta bayyana taimakon da ya yi mata a baya

  • Kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah, ta sanar da cewa dari bisa dari ta ke bayan Tinubu a burin sa na mulkar kasar nan a 2023
  • Shugabannin kungiyar sun yi taro a Abuja, kuma mashiryin taron Ya'u Haruna ya sanar da yadda Tinubu ya taimaka wa kungiyar yayin da ya ke gwamnan Legas
  • Ya tabbatar da cewa, matukar zai iya wannan taimakon na sasanta su a jihar Binuwai, abinda zai yi kuwa idan aka zabe shi shugaban kasa sai ya fi hakan

FCT, Abuja - Kungiyar Miyetti Allah, MACBAN, ta bayyana goyon bayan ta ga jigon jam'iyyar APC, Bola Tinubu, kan burin sa na zama shugaban kasan Najeriya a zaben 2023 mai gabatowa.

Shugabannin Fulanin sun sanar da hakan ne a wani taro da suka yi a cibiyar horarwa tare da kula da noma da kiwo da kuma habaka karkara da ke Abuja a ranar Lahadi, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Takarar shugaban kasa a 2023: Babatu 3 da Tinubu ya yi da ka iya sa ya fadi a 2023

2023: Miyetti Allah ta ce ta na bayan Tinubu, ta bayyana taimakon da ya yi mata a baya
2023: Miyetti Allah ta ce ta na bayan Tinubu, ta bayyana taimakon da ya yi mata a baya. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, taron ya samu halartar shugabannin Fulani na jihohi talatin da shida da babban birnin tarayya.

Mashiryin taron kuma tsohon shugaban MACBAN na jihar Jigawa, Ya'u Haruna, ya yi bayanin cewa ana ta wayar da kan yankunan Fulani kafin zuwan zaben 2023 a kan tsaro da kuma yadda za a zauna lafiya da juna har da makwabta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

"Masu iko sun kwace da yawa daga cikin burtalin mu, idan kuwa muna son kayan mu, dole ne mu shiga siyasa kuma mu nemi mukaman siyasa.
"A halin yanzu, muna kokarin wayar wa jama'a kai tunda yanzu da yawansu suna da katinan zabe kuma muna jiran lokacin zabe.
“Muna cigaba da tantance masu burin shugabancin kasa kuma Bola Tinubu ne kan gaba a wurin mu saboda ya taba shiga lamarin mu a baya yayin da ya ke gwamnan jihar Legas lokacin da muka samu rikici a Binuwai.

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sa zan nemi takarar kujerar Buhari a 2023 – Tsohon gwamnan Zamfara

“Tinubu da kan shi ya zo, ya hada mu tare da yi mana sasanci. Toh gaskiya duk wanda yayi hakan a wancan lokacin, mun yarda cewa zai iya yin fiye da hakan a al'amuran mu," Haruna yace.

Shugaban MACBAN din ya jajanta yadda ake kallon Fulani a Najeriya a matsayin 'yan ta'adda duk da yawancin su mutanen kwarai ne.

Ortom ga FG: Ku ayyana Miyetti Allah a matsayin kungiyar ta'addanci

A wani labari na daban, gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya ayyana kungiyar makiyayan shanu ta Miyetti Allah, MACBAN, a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda.

Kiran ya biyo bayan yadda gwamnatin tarayya ta ayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda, TheCable ta ruwaito.

A wata takarda wacce sakataren watsa labaran gwamnan, Nathaniel Ikyur ya saki, ya yanko inda gwamnan ya ce kungiyar tana kawo tashin hankali a Binuwai.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Najeriya ba ta buƙatar shugaban ƙasa na ƙabilanci, Hakeem Baba-Ahmed

Asali: Legit.ng

Online view pixel