Na gwammaci yashe teku: Cece-kuce yayin da budurwa ta rokon saurayi ya aureta

Na gwammaci yashe teku: Cece-kuce yayin da budurwa ta rokon saurayi ya aureta

  • Cece-kucen 'yan soshiyal midiya ya biyo bayan wani faifan bidiyo da aka ga wata budurwa tana neman saurayi ya aureta
  • Yayin da budurwar ta durkusa da gwiwowinta da zobe, sai mutumin ya mika hannunsa don nuna amincewarsa da auren ta
  • Sai dai wannan kyakkyawan shauki na soyayya bai yi wa wasu masu 'yan soshiyal midiya dadi ba wadanda ke ganin shiri ne kawai

Kararrawar bikin aure na kadawa wata baiwar Allah wacce saurayunta ya amince da bukatar aurenta. Budurwar ta cire tsoro ta yi abin da ya dace, inda ta ba saurayinta zoben alkawari.

A cikin wani bidiyon da @instablog9ja ya yada a Instagram, an ga budurwar ta durkusa a gaban saurayin. Nan take ya mika hannunsa na hagu don karbar zoben aurenta.

Mace mai neman na aure
Na gwammace na yashe teku: Cece-kuce yayin da budurwa ta rokon saurayi ya aureta | Hoto: @instablog9ja
Asali: Instagram

Budurwar ta mike, inda suka hade tare da sumbatar juna. Amma wannan lamari fa ya jawo hankali sosai a kafar Instgram, tare da mutane da yawa ba su yarda da hakan gaske ya faru ba.

Kara karanta wannan

Takarar shugaban kasa a 2023: Babatu 3 da Tinubu ya yi da ka iya sa ya fadi a 2023

Wasu sun ce hakan bai kamata ba, cewa ba daidai ba ne, amma wasu sun ce a bar ma'auratan su ji dadin .yuwarsu, kowa da kaddararsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Martanin 'yan soshiyal midiya

Mun tattaro muku kadan daga martanin 'yan Instagram:

@domingo_loso:

"Matar gobe don Allah kar ki yi haka. Nine zan yi hakan, ya kamata mu kiyaye daidaitattun al'adu."

@bbree5:

"Mutumin ya karba ne don kada ta ji kunya."

@milly_posh21:

"Mutumin ko bata lokaci bai yi ba. Da alama dama yana tsammani hakan."

@olaedoamarachi:

"Mutumin ya karba ne saboda ya riga ya yanke shawarar yin rayuwar shi da ita..In ba haka ba, ba zai yarda ba. #Na taya su murna."

@tianareginald:

"Amma dakata fa, mutum zai nemi aure ne idan ya san ya shirya a hankalce, da kudi, to idan mace ta nemi aure ita ce za ta sanya ranar daurin aure, ta biya ango sadaki, ta biya kudin shagalin auren? Na rude gaskiya?, ka manta da farkawa! Neman aure ga namiji A'A da A'A ne don Allah."

Kara karanta wannan

Karya ne: NEC ba ta kai ga kara kudin man fetur daga N165 zuwa N300 ba - Osinbajo

Baturiya mai auren ‘Dan Najeriya ta rangada ado, ta ci ankon atamfa da yara da mai gidanta

A wani labarin, wata mutumiyar kasar Switzeland da ke auren ‘dan Najeriya, ta dandasa gayun da ya jawo masu bibiyar kafofin sada zumunta suke ta magana.

Wannan Baiwar Allah da aka sani da Nwanyi Ocha, tayi shiga ne kamar asalin ‘yar Najeriya.

Kamar yadda Legit.ng ta kawo rahoto, Nwanyi Ocha ta dinka atamfa, ta sa zuwa wajen jana’izar Mai martaba Sarkin kasar Isuofia, Cif Agbazue.

Cif Agbazue shi ne yake sarautar kauyen Isuofia inda mai gidanta ya fito. Baturiyar da ke surukuntaka da Najeriya, ta halarci jana’izarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel