2023: Za mu bi didigin inda ƴan takara suke samo kuɗi, za mu sa ido kan asusun bankin ƴan siyasa, INEC

2023: Za mu bi didigin inda ƴan takara suke samo kuɗi, za mu sa ido kan asusun bankin ƴan siyasa, INEC

  • INEC ta aike da muhimmin sako ga yan siyasa da ke neman tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023
  • Hukumar mai zaman kanta ta ce saboda zaben shekarar 2023, za ta saka idanu a kan asusun bankunan yan siyasa
  • Har wa yau, INEC ta ce za ta samar da jami'ai da za su rika saka idanu a kan yadda ake tura kudade yayin zabe don hana siyar kuri'a

FCT, Abuja - Hukumar zabe mai zaman kanta na Najeriya, INEC, ta aika da muhimmin sako ga yan siyasa da jam'iyyun siyasa gabanin babban zaben shekarar 2023.

Hukumar ta sha alwashin cewa za ta saka idanu a kan 'yan siyasa da jam'iyyun siyasa domin gano inda suke samo kudade domin yakin neman zabe, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sa zan nemi takarar kujerar Buhari a 2023 – Tsohon gwamnan Zamfara

2023: Za mu bi didigin inda ƴan takara suke samo kuɗi, za mu sa ido kan asusun bankin ƴan siyasa, INEC
INEC: Za mu bi didigin inda yan siyasa ke samo kudade, za mu saka ido a asusun bankunansu. Hoto: INEC Nigeria
Asali: Facebook

Shugaban INEC na kasa, Farfesa Mahmood Yakubu, wanda ya bayyana hakan yayin wani taro da hukumar zaben ta shirya a Abuja, ranar Juma'a 21 ga watan Janairu, kuma ya ce hukumar za ta saka ido kan yadda aka hada-hadar kudade ranar zabe don dakile siyan kuri'u, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban na INEC da ya samu wakilcin Farfesa Ajayi Kunle, kwamishinan INEC mai kula da kwamitin saka idanu kan sa idanu ya ce:

"Za mu kafa tawaga masu sa ido kuma za su kasance cikin masu zabe amma su (yan siyasan da jam'iyyun siyasa) ba za su sani ba."

2023: Zan iya shugabancin Najeriya amma dai ban matsu ba, Orji Kalu

A wani labarin, bulaliyar Majalisar Dattawa, Orji Uzor Kalu, ya ce duk da a shirye ya ke da ya yi kamfen kuma zai iya shugabantar kasar nan, amma bai matse ya ce ai zama shugaban Najeriya ba, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2023: Tsohuwar Sanata ta aika saƙo mai tada hankali ga Tinubu, Osinbajo, Atiku da sauran ƴan takara

Kalu, tsohon gwamnan Jihar Abia, ya yi wannan bayanin ne a ranar Laraba yayin amsa tambayoyi daga manema labarai a Majalisar Tarayya, washegarin da ya kai wa Buhari ziyara a fadarsa da ke Abuja.

A cewarsa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, takarar shugaban kasa hukunci ne ‘yan Najeriya zasu yanke sannan ko wacce jam’iyya zata zabi bangaren da za ta bai wa damar tsayawa takara, musamman jam’iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel