'Yan Najeriya na son Jonathan ya dawo mulki, In ji tsohon kwamishina

'Yan Najeriya na son Jonathan ya dawo mulki, In ji tsohon kwamishina

  • Mr Moses Essien, Tsohon Kwamishinan Ilimi a Jihar Akwa Ibom ya ce 'yan Najeriya suna son tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya dawo mulki
  • Shugaban na kungiyar yakin neman zaben Goodluck Jonathan na kasa ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis 20 ga watan Janairu
  • Essien ya ce ayyuka masu kyau da adalci da GEJ ya yi a lokacin mulkinsa ne yasa 'yan Najeriya suke son ya dawo kan karagar mulki a shekarar 2023

Akwa Ibom - Tsohon Kwamishinan Ilimi a Jihar Akwa Ibom, Mr Moses Essien, ya ya ce 'yan Najeriya suna son tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan ya dawo ya jagoranci kasar, The Punch ruwaito.

Essien, wanda shine shugaban kungiyar yakin neman zaben Goodluck Jonathan ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Najeriya ba ta buƙatar shugaban ƙasa na ƙabilanci, Hakeem Baba-Ahmed

'Yan Najeriya na son Jonathan ya dawo mulki, In ji tsohon kwamishina
Tsohon kwamishina ya ce 'yan Najeriya suna son Jonathan ya dawo. Hoto: The Punch
Asali: Depositphotos

Ya ce:

"Masu iya magana na cewa, haja mai kyau yana siyar da kansa, domin yana da kyau, da kansa zai rika sayar da kansa. Wannan shine abin da muka gani game da tsohon Shugaba Goodluck Jonathan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Najeriya tana kan wani gaba mai muhimmanci da ya shafi hadin kanta da tarihi. Kasar na bukatar mutum mai gaskiya da zai ceto ta, mara kabilanci da zai gina kasar bisa tsarin demokradiyya. Wannan shine abin da GEJ zai kawo kasar nan.
"Idan ka yi wa abin kallo daga kasa baki daya, za ka gano cewa ba arewa kadai bane, kowanne yanki na kasar ya kosa kuma yana neman masoyinsu GEJ ya dawo kan mulki."

Rahoton ya cigaba da cewa Essien ya kara da cewa tsohon shugaban kasar mutum ne mai gaskiya da adalci, yana mai cewa ya nuna hakan a lokacin da ya ke shugabancin Najeriya.

Kara karanta wannan

Matsalar Tsaro: Baicin kwarewar Buhari, da Najeriya ta ruguje kurmus

Essien ya ce:

"Ya yi wa kowa adalci, musamman arewa, ta amfana daga adalcin gwamnatin GEJ. Misali, a bangaren ilimi, wanda ya ke da muhimmanci, GEJ ya bar manyan-manyan ayyuka da arewacin Najeriya a matsayinsa na shugaba."

2023: Zan iya shugabancin Najeriya amma dai ban matsu ba, Orji Kalu

A wani labarin, bulaliyar Majalisar Dattawa, Orji Uzor Kalu, ya ce duk da a shirye ya ke da ya yi kamfen kuma zai iya shugabantar kasar nan, amma bai matse ya ce ai zama shugaban Najeriya ba, Daily Trust ta ruwaito.

Kalu, tsohon gwamnan Jihar Abia, ya yi wannan bayanin ne a ranar Laraba yayin amsa tambayoyi daga manema labarai a Majalisar Tarayya, washegarin da ya kai wa Buhari ziyara a fadarsa da ke Abuja.

A cewarsa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, takarar shugaban kasa hukunci ne ‘yan Najeriya zasu yanke sannan ko wacce jam’iyya zata zabi bangaren da za ta bai wa damar tsayawa takara, musamman jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan

Yadda Abacha ya yaudari yan siyasa ya dane kujerar shugaban kasa, Janar IBB

Asali: Legit.ng

Online view pixel