Yadda Abacha ya yaudari yan siyasa ya dane kujerar shugaban kasa, Janar IBB

Yadda Abacha ya yaudari yan siyasa ya dane kujerar shugaban kasa, Janar IBB

  • Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya yi waiwaye kan abinda ya faru lokacin da ya nada gwamnatin rikon kwarya a 1993
  • Yan watanni bayan sauka daga mulki, Janar Abacha ya yiwa Ernest Shonekan juyin mulki
  • Janar Abacha ya mulki Najeriya daga 1993 zuwa 1998 da Allah ya dauki ransa

Minna - Tsohon Shugaban kasan mulkin Soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, wanda aka fi sani da IBB Maradona ya bayyana yadda marigayi Janar Sani Abacha ya dane karagar mulki.

A hirarsa da Trust TV, IBB ya ce Abacha yaudarar yan siyasa da yan fafutuka yayi don zama Shugaban kasa.

IBB ya bayyana cewa marigayi Abacha babban abokinsa ne.

Yadda Abacha ya yaudari yan siyasa ya dane kujerar shugaban kasa, Janar IBB
Yadda Abacha ya yaudari yan siyasa ya dane kujerar shugaban kasa, Janar IBB
Asali: Getty Images

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Yayinda aka kashe mutum 220 a jihar Neja, Buhari yayi Allah wadai da harin da aka kai Kasar Dubai

Abacha ya kasance Shugaban hafsan Sojin Najeriya karkashin IBB, daga baya kuma ya nada shi Ministan tsaro a 1990.

Ya mulki Najeriya sakamakon juyin mulkin da ya yiwa Ernest Shonekan a 1993.

IBB yace:

"Gwamnatin Abacha mai wayau ce. Sun san wadanda ke hakikancewa kan zabe, juyin mulki, June 12 dss. Sai suka yaudaresu ta hanyar fada musu idan aka cire gwamnatin dake rikon kwarya, za'a dawo da mulkin demokradiyya gaba daya."
"Sun yaudari al'umma da wasu manyan mutanen gari, kuma bayan Abacha ya dane mulki, suka rika wasa da hankalin mutane cewa lokaci yayi, za'a nada gwamnatin demokradiyya."
"Na sani sarai karya ce saboda ta yaya zan sanya rayuwata cikin hadari kuma in mika muku mulki? Abinda ya faru kenan."

IBB: Mu waliyyai ne akan 'yan siyasar yanzu idan ana maganar rashawa

Ibrahim Badamasi Babangida, ya ce idan aka kwatanta yawan cin hanci da rashawa da ke yi a Najeriya yanzu, toh su waliyyai ne a lokacin da yake mulki.

Kara karanta wannan

Zamfara APC: Rikici ya dauka sabon salo, ana amfani da 'yan daba wurin kai farmaki

Ya ce a lokacin da yake kan mulki, ya tsige gwamna saboda badakalar N300,000 amma sai ga shi a yanzu yan siyasa na yin sama da fadi kan biliyoyin naira hankali kwance.

Yace ya sallami gwamna saboda badakalar N300,000.

A cewarsa, yanzu akwai mutane da muke karantawa a jaridu wadanda suke satar naira biliyan 2, naira biliyan 3.

Asali: Legit.ng

Online view pixel