Matsalar Tsaro: Baicin kwarewar Buhari, da Najeriya ta ruguje kurmus

Matsalar Tsaro: Baicin kwarewar Buhari, da Najeriya ta ruguje kurmus

  • Gwamnan jihar Cross River ya bayyana yadda kasancewar Buhari tsohon Soja ya taimakawa yan Najeriya wajen dakile matsalar tsaro
  • Ayade ya ce bai cin kwarewar Shugaba Buhari, da tuni Najeriya ta ruguje saboda akwai makyarkashiya da ake shiryawa
  • Ayade ya yi kira ga yan Najeriya su zama tsintsiya madaurinki daya wajen fuskantar kalubale

Calabar - Gwamna Ben Ayade na jihar Cross Rivers ya jinjinawa shugaba Muhammadu Buhari bisa kokarin da yake wajen magance matsalar rashin tsaro a Najeriya.

A cewarsa, da Najeriya ta dade da rugujewa baicin kokarinsa.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a shirin Sunrise Daily an ChannelsTV ranar Laraba, inda ya yi bayanin yadda kasancewar Shugaban kasa tsohon Soja ya taimaka.

A cewarsa, akwai wani makyarkashiya da kasashen waje ke yiwa Najeriya, musamman Arewa.

Kara karanta wannan

Yayinda aka kashe mutum 220 a jihar Neja, Buhari yayi Allah wadai da harin da aka kai Kasar Dubai

"La'lla, baccin gwamnatin Buhari da kasancewarsa Soja, da Najeriya ta ruguje yanzu," ya kara.

"Mutane basu fahimci haka ba saboda idan ka kawar da wani mugun abu, babu wanda ke iya gani. Amma da abubuwa sun fi haka muni."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Matsalar Tsaro: Baicin kwarewar Buhari, da Najeriya ta ruguje kurmus
Matsalar Tsaro: Baicin kwarewar Buhari, da Najeriya ta ruguje kurmus Hoto: Presidency

Ya ce bayan magance matsalar rashin tsaro, gwamnatin yau ta farfado da tattalin arziki, kuma an yi yunkurin samar da wasu sabbin hanyoyin samar da kudin shiga.

"A yau, gwamnatin APC na shirin fito da wani babban shiri. Muna da ton bilyan 42 na arzikin bitumen a Najeriya, mune na uku bayan kasar Canada Venezuela a duniya. Wannan gwamnatin na da babban shiri wajen samar da masana'antar sarrafa bitumen da babu a baya," gwamnan ya kara.

Gwamnan, wanda ya godewa jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP) bisa lokacin da yayi a jam'iyyar adawar, ya yi kira da su baiwa gwamnati shawara lokacin da ya kamata.

Kara karanta wannan

Mutum daya ya mutu sakamakon gardama kan Chelsea da Barcelona a Katsina

A cewarsa, yan Najeriya su ajiye siyasa a gefe kuma a kaddamar da cigaban kasa a duk abinda suke yi.

"Ba zan so in yi magana kan lamarin siyasa ba saboda siyasa ce ta mayar da kasar koma baya. Mu yi tunani a matsayin kasa; muyi tunani a matsayin jama'a guda," tsohon dan PDP ya fada.

"Babu wata matsalar da gwamnatin PDP ke da ita, yan PDP na bada gudunmuwa wajen cigaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel