Gwamnatin Amurka ta gurfanar da mutum 8 da ake zargi sun shirya kashe shugaba Donald Trump, mataimakinsa, Netanyahu, Elon Musk da wasi jami'an Amurka.
Gwamnatin Amurka ta gurfanar da mutum 8 da ake zargi sun shirya kashe shugaba Donald Trump, mataimakinsa, Netanyahu, Elon Musk da wasi jami'an Amurka.
Malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum ya gargadi masu masa kirari da likitan zuciya da sauransu. Ya ce ba ya jin dadin hakan.
Rundunar sojin Najeriya da hadin gwiwar DSS sun kama makamai ana shirin shigoawa da su Najeriya daga kasar Nijar. An kama motar a Kaura Namoda a Zamfara.
Yayin da ake ta ce-ce-ku-ce kan raba awaki, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kare shirin yana cewa naman awaki na da amfani sosai wajen magance cututtuka.
Dan takarar gwamnan jihar Edo a karkashin inuwar jam'iyyar PDP, Dr. Asue Ighodalo, ya shigar da mukaddashin shugaban APC na jihar kara a gaban kotu.
Kotun Kano ta hana kama Muhuyi Magaji Rimingado, yayin da 'yan sanda suka fayyace cewa ba kama shi suka yi ba, an gayyace shi ne kawai domin bincike.
Wasu 'yan daba sun lakada wa wata jami'ar Hukumar Tsaro ta NSCDC duka har ta fadi sumammiya a jihar Kwara yayin da ake bikin nadin sarauta a birnin Ilorin.
Wasu majiyoyi masu karfi sun musanta rahotanni da ke cewa wai rundunar sojojin Nigeriya ta yi nasarar cafke rikakke kuma shugaban yan ta'adda, Bello Turji.
Hukumar tattara kudin shiga ta jihar Kano (KIRS) ta garƙame otal ɗaya da waus kamfanoni 4 saboda sun yi wa gwamnatin tsaurin ido, sun ƙo biyan harajin da ake binsu.
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta yi magana kan rahotannin da ke cewa ta cafke shugaban hukumar kula da korafe-korafen jama'a da yaki da cin hanci na Kano.
Wasu 'yan Izala a kafafen sada zumunta sun yi rubdugu da shugaban malaman Izala, Dr Ibrahim Jalo Jalingo kan bikin Qur'anic Festival da aka shirya a Abuja.
Labarai
Samu kari