'Yan Sanda Sun Gamu da Matsala: Kotun Kano Ta Yi Hukunci kan Kama Muhuyi Magaji
- Wata babbar kotu ta hana 'yan sanda kamawa ko gayyatar shugaban hukumar rashawa ta jihar Kano, Muhuyi Magaji Rimingado
- Wannan na zuwa ne yayin da rundunar ‘yan sanda ta ce ba kama Muhuyi ta yi ba, ta gayyace shi ne domin amsa tambayayi
- Mai shari’a Sunusi Ado Ma’aji na babbar kotun jihar Kano ya yanke hukuncin da zai zama cikas ga yi wa Muhuyi Magaji tambayoyi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Babbar kotun kano karkashin Mai shari’a Sunusi Ado Ma’aji ta bayar da umarnin wucin-gadi kan hana kamawa ko gayyatar Muhuyi Magaji Rimingado.
Kotun ta hana Sufeto Janar na 'yan sanda da sauran hukumomin tsaro tsangwamar shugaban hukumar karɓar korafe-korafe da yaki da rashawa ta Kano.

Asali: Facebook
Gwamnatin Kano ta yi karar 'yan sanda
Masu gabatar da ƙara sun haɗa da Antoni Janar na jihar Kano, hukumar karɓar korafe-korafe da yaki da rashawa ta Kano, da kuma Rimingado, inji rahoton Channels.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wadanda ake ƙara sun haɗa da rundunar ‘yan sandan Najeriya, Sufeto Janar, AIG na shiyya ta daya, da kwamishinan 'yan sandan Kano.
Sauran wadanda ake kara a wannan shari'ar sun hada da ASP Ahmed Bello da Bala Muhammad Inuwa.
Umarnin kotun, wanda aka bayar ranar Litinin, ya hana waɗanda ake ƙara ko wakilansu yin karan tsaye ga haƙƙoƙin masu gabatar da ƙara na biyu da na uku.
Hukuncin da kotu ta yanke kan Rimingado
Mai shari’a Ma’aji ya ce:
“Waɗanda ake ƙara ba su da hurumin gayyata, kamawa, ko tsare jami’an masu gabatar da ƙara na biyu.
“An kuma hana waɗanda ake ƙara tsoma baki cikin harkokin masu gabatar da ƙara na biyu da na uku gaba ɗaya."
Kotun ta kuma hana ‘yan sanda tilasta wa Rimingado halartar kowanne ofishinsu, ciki har da hedikwatar Abuja, har sai an warware batun.
'Yan sanda sun karyata Muhuyi Magaji

Kara karanta wannan
Kudiri yayi nisa a majalisa, Gwamna Abba zai kafa hukumar tsaro mallakin jihar Kano
Wannan na zuwa ne yayin da rundunar ‘yan sanda ta ƙaryata ikirarin Rimingado na cewa an kama shi, tana mai bayyana hakan a matsayin "kanzon kurege."
Rundunar ta bayyana hakan a wata sanarwa da mai magana da yawunta, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya fitar domin fayyace matsayinta.
Sanarwar ta ce:
“Muna so mu fayyace cewa ba a kama Muhuyi ba, an dai gayyace shi ne domin amsa ƙorafin da aka shigar a kansa.”
Kotun ta dage sauraron ƙarar har zuwa lokacin da za a ci gaba da shari’ar.
"Za mu binciki Ganduje" - Muhuyi Magaji
A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar karɓar korafe-ƙorafe da yaki da rashawa ta Kano (PCACC) ta ce za ta ci gaba da shari’ar da ta shafi Abdullahi Ganduje.
Ana tuhumar tsohon gwamnan Kano da almundahana, rashawa, handame kuɗin jama’a, da karkatar da dukiyar kasa ba bisa ka’ida ba.

Kara karanta wannan
Rigima ta kunno kai a Kudu kan kafa shari'ar Musulunci, an gano inda matsalar take
Shugaban hukumar, Barista Muhuyi Magaji Rimingado, ya tabbatar da cewa ba za a dakatar da binciken da ake yi kan Ganduje ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng