Abba Gida Gida Ya Nada Sababbin Mukamai, An Sauya wa Wasu Wurin Aiki a Kano
- Gwamnatin Kano ta nada kwararriyar ma’aikaciyar kudi da gogewa fiye da shekaru 16 domin kula da harkokin baitul mali
- An nada Injiniya Abubakar Sadiq a matsayin Mataimakin Darakta Janar na Hukumar Samar da Ruwa da Tsaftar Muhalli a Kauyuka
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa an yi sabbabin nade-naden domin inganta harkar gudanar da gwamnatin jihar
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da wasu muhimman nade-nade na domin tafiyar da gwamnatin jihar.
Gwamnan ya kuma yi wasu sauye-sauye a bangarori masu muhimmanci don hanzarta ci gaba da bunkasa jihar Kano.

Asali: Facebook
An sanar da sabbin nade-naden sun fito ne cikin wata sanarwa Darakta Janar a kan yada labarin gwamnatin Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta bayyana cewa nade-naden manuniya ce ga aniyar wannan gwamnati na aiki da kwararru masu hazaka da gogewa mukamai masu muhimmanci domin su ja ragamar ci gaba.
Gwamnan Kano ya yi muhimman nade-nade
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi nade-nade hudu a bangarori daban-daban na jihar. wadanda aka nada sun hada da:
1. An nada sabuwar Akanta Janar
Jamila Magaji Abdullahi, kwararriyar ma’aikaciyar harkokin kudade da haraji ce da ta gogewa fiye da shekaru 16.
Ta yi karatun digiri a fannin Akanta da digiri na biyu a bangaren kula da baitul mali daga Jami’ar Bayero, Kano.
A baya, ta rike mukamai a Hukumar Haraji ta Tarayya (FIRS) da Ma’aikatar Kudi ta Jihar Kano, inda ta samu gogewa da kwarewar da za su taimaka mata wajen tafiyar da harkokin kudin jihar cikin kwarewa da amana.
Jamila Magaji Abdullahi, ‘yar asalin karamar hukumar Dawakin Tofa ce, kuma ita ce tsohuwar Daraktar Akanta a Ma’aikatar Kudi ta Jihar Kano.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Kano ta yi kuskuren ingiza wa wani jami'inta maƙudan kuɗi, ya dawo da su
2. Muhammad Yahaya Liman – Daraktan Akanta
Muhammad Yahaya Liman, kwararren ma’aikacin banki ne kuma masanin harkokin kudi mai gogewa fiye da shekaru 16, ya kware wajen bayar da rahotannin kudi.
Ya yi karatun digiri a fannin Accounting, digiri na biyu a Finance and Investment, da kuma digiri na uku a Accounting and Financial Management daga Jami’ar Bayero, Kano.
3. An yi sabon nadi a gwamnatin Kano
An kara wa Akibu Isa Murtala girma daga mukaminsa na Babban Mataimaki na Musamman a Ofishin Shugaban Ma’aikata zuwa Mai Ba da Shawara na Musamman kan Harkokin Gudanarwa.
Wannan mukami yana nuna kwarewarsa da jajircewarsa wajen tabbatar da aiwatar da ayyukan gwamnati ba tare da tangarda ba.
4. Gwamnati ta yi nadi a RUWASA
An sauya Injiniya Abubakar Sadiq daga mukaminsa na Mataimakin Darakta Janar na Kano Line zuwa RUWASA.
Gwamnati ta ce ta yi sauyin ne domin ya dace da aniyarta na magance matsalolin muhalli da inganta rayuwar al’ummar karkara ta hanyar samar da ingantaccen ruwa da tsaftar muhalli.
An yi bayanin jami'in gwamnatin Kano
A baya, kun ji cewa rundunar ‘yan Sandan Najeriya ta yi karin haske kan zargin da aka yi cewa ta cafke shugaban Hukumar Kula da Korafe-Korafen Jama’a da Yaki da Cin Hanci ta Jihar Kano, Muhuyi Magaji Rimingado.
A wata sanarwa da jami'in hulda da jama'a na rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya fitar a ranar Litinin, ya bayyana cewa ba a cafke Muhuyi Magaji ba, sai dai kawai an gayyace shi domin amsa tambayoyi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng