Fadar shugaban kasa ta yi tsokaci kan batun ma'aikatar bogi da ake ta cece-kuce . Ta umarci hukumomin DSS da EFCC su gudanar da bincike kan lamarin
Fadar shugaban kasa ta yi tsokaci kan batun ma'aikatar bogi da ake ta cece-kuce . Ta umarci hukumomin DSS da EFCC su gudanar da bincike kan lamarin
Rahotanni sun nuna cewa barci ya dauke wasu 'yan bindiga masu garkuwa da mutane bayan sace wasu jama'a, inda jama'ar suka tsere suka gudu daga dajin.
Kungiyar kwadago ta yi Allah wadai da karin kudin wuta da gwamnatin Najeriya ke shirin yi. NLC za ta rufe Najeriya kirif da yin zazzafar zanga zanga ga Bola Tinubu.
Jam'iyyar APC ta dakatar da Ƙabir Sani Giat, mao ba gwamnan Kebbi, Nasir Idris shawara kan harkokin siyasa da makamashi kan shiga da maciji gidan gwamnati.
Kungiyar Kiristoci a Najeriya, CAN ta bukaci jihohin Bauchi, Katsina, Kano da Kebbi su janye matakin rufe makarantu na makonni biyar don azumin Ramadan.
Gwamna Fubara ya bada umarni cewa shugabannin kananan hukumomi su mika mulki, yayin da Kotun Koli ta hana Ribas samun kudaden gwamnati daga CBN da Akanta Janar.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an birne Sarkin Sasa, Haruna Maiyasin Katsina, wanda ya rasu yana da shekara 125, a gidansa da ke Sasa, Ibadan, Oyo a yau Lahadi.
‘Yan sandan jihar Imo sun kama masu safarar yara, inda suka ki karbar cin hancin N1m, kuma suna ci gaba da bincike kan wata babbar cibiyar safarar yara.
Hukumar Hisbah ta cafke wasu matasa da ake zargi da rashin yin azumi a ranar farko ta watan Ramadan. Jami'an hukumar sun kuma kama masu askin banza.
Makinde ya jajanta wa iyalan Sarkin Sasa, yana mai cewa rasuwarsa babban rashi ne ga al’ummar Hausa/Fulani, ya kuma yi masa addu’ar samun Aljanna Firdausi.
Wata coci a jihar Kaduna ta tuna da al'ummar musulmai yayin da suka fara azumin watan Ramadan. Cocin ta raba kayayyakin abinci ga mutane mabukata.
Labarai
Samu kari