'Yan bindiga dauke da makamai sun kai wani harin ta'addanci a jihar Sokoto. 'Yan bindigan sun kashe wani babban limami tare da sace matan aure yayin harin.
'Yan bindiga dauke da makamai sun kai wani harin ta'addanci a jihar Sokoto. 'Yan bindigan sun kashe wani babban limami tare da sace matan aure yayin harin.
Hadimin shugaban kasa, Bayo Onanuga ya ce matsalar tsaron Najeriya bata kai yadda mutane ke yawan fadan ta ba. Ya ce mutane na ruruta matsalar tsaro.
Matatar man hamshakin ɗan kasuwa, Aliko Ɗangote ta rage farashin fetur a karon farko bayan gangar mai ta sauka sakamakon tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Iran.
Wasu fusatattun matasa sun ɓarke da zanga zanga kam yawaitar hare-haren ƴan bindiga a garin Lafiagi, ƙaramar hukumar Edu a jihar Kwara, sun nemi tsaro.
Gwamna Abdulrazaq na jihar Kwara ya maka tsohon ɗan Majalisar tarayya, Moshood Mustapha, da ɗan'uwansa a kotu kan zargin wallafa bidiyon da zai tunzura jama'a.
Jirgin sama mallakin kamfanin Rano Air ya samu matsala a injinsa bayan ya tashi da nufin zuwa Katsina daga Abuja, hukumar NCAA ta bada umarnin bincike.
'Yan sanda sun kama masu garkuwa da mutane uku kuma sun ceto mutane 29 a Kogi, Legas, da Katsina, a wani samame na musamman kan yaƙi da miyagun laifuffuka.
Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da cewa an ɗage jana'izar marigayi Alhaji AminuƊantata zuwa gobe Talata a birnin Madina saboda cika sharuɗdan Saudiyya.
A labarin nan, za a ji cewa sojojin Najeriya sun yi amfani da bayanan sirri wajen dakile mummunan hari da 'yan ta'addan ISWAP ke kokarin kai wa Borno.
Rahatanni daga jihar Zamfara sun nuna cewa jami'an tsaro sun yi nasarar halaka kasurgumin ɗan bindiga da ya takura wa jama'a, Kachalla Yellow Ɗanbokolo.
A labarin nan, za a ji cewa PDP na iya fuskantar babbar barazana yayin da gwamnoni da sauran masu ruwa da tsaki a Kudu maso Gabas ke barazanar ficewa.
Labarai
Samu kari