'Yan ta'addan Boko Haram dauke da makamai sun kai hari a wasu makarantu da ke jihar Borno. Ana fargabar cewa 'yan ta'addan sun sace dalibai da dama.
'Yan ta'addan Boko Haram dauke da makamai sun kai hari a wasu makarantu da ke jihar Borno. Ana fargabar cewa 'yan ta'addan sun sace dalibai da dama.
Atiku Abubakar ya ce Yarbawa za su zama ginshiƙi a gwamnatinsa idan ya zama shugaban kasa a 2027, yana mai karyata rade radin da ake yadawa cewa zai fifita Fulani.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya shiga ganawa da tsohon shugaban riko na jihar Ribas, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), ministan kudi da shugaban EFCC.
Gwamnatin jihar Bauchi karkashin jagorancin Gwamna Bala Mohammed ya sallami wasu manyan jami'ai biyu daga aiki bisa laifin amfani da takardun bogi.
Hukumar binciken hadurra ta NSIB ta gano cewa rashin ingantaccen gyara da matsalar na'ura ne suka haddasa hatsarin jirgin kasa a tashar, hanyar Abuja–Kaduna.
An yi rashi na wani fitaccen dan kasuwa a Najeriya. Olorogun Oscar Ibru ya yi bankwana da duniya. Ya rasu ne sakamakon wata cuta da ba a bayyana ba.
Tsohon dan takarar shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya tabbatar da rasuwar abokinsa na yarinta, MB Suleiman Jada, ya aika sakon ta'aziyya ga iyalansa.
Wani jirgin sama na kamfanin Ibom Air ya yi gaggawar komawa filin jirgin da ya tashi a Abuja sakamakon tsananin rashin lafiyar daya daga cikin fasinjojinsa.
Dan majalisar dokokin jihar Plateau da 'yan bindiga suka yi garkuwa da shi ya shaki iskar 'yanci. Dan majalisar ya kubuta ne bayan an sace shi a gidansa.
Wasu da ake zargin yan damfara ne sun yi wa shafin yanar gizo na ma'aikatar ilimin Najeriya kutse, sun wa'lafa wata takarda ta tallafin karatu a kasar Rasha.
Labarai
Samu kari