Cigaba: Najeriya Ta Fara Fitar da Kayan Sola da Ta Kera zuwa Ketare

Cigaba: Najeriya Ta Fara Fitar da Kayan Sola da Ta Kera zuwa Ketare

  • Najeriya ta fara fitar da kayan sola da aka kera cikin gida zuwa Ghana domin fadada kasuwancin makamashi a yankin Afrika ta Yamma
  • Ministan makamashi na kasa, Bayo Adelabu, ya bayyana cewa hakan na nuna matsayin Najeriya a kasuwar makamashi a nahiyar Afrika
  • Ya kara da cewa matakin na zuwa ne bayan Najeriya ta kera sabuwar cibiyar samar da makamashi mai karfin gigawatt hudu a shekara

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Lagos – Rahoto ya nuna cewa Najeriya ta fara fitar da kayan sola da aka kera cikin gida zuwa ƙasar Ghana.

Gwamnatin kasar ta ce hakan ya zama alamar cigaba a yunkurin ƙasar na zama cibiyar habaka makamashi a yankin Afrika ta Yamma.

Shugaba Bola Tinubu
Hoton wasu masu hada sola da shugaba Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga|Getty Images
Source: UGC

Business Day ta wallafa cewa ministan makamashi, Bayo Adelabu, ne ya bayyana hakan a taron Nigeria Energy Forum 2025 da aka gudanar a birnin Lagos.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya ce an yi abin kunya a filin wasan Kebbi da aka gina da kudin FIFA

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Najeriya na fitar da kayan sola waje

Adelabu ce wannan ne karon farko da Najeriya ke shiga kasuwar makamashi ta yankin, bayan kaddamar da sabuwar cibiyar kera kayan sola mai karfin samar da gigawatt hudu a shekara.

Ministan ya ce:

“Da irin wannan cigaba a kera makamashi mai aiki da hasken rana, bayan cimma burin ta na sauya tsarin makamashin cikin gida, Najeriya za ta iya samar wa kasashen makwabta makamashi, kamar yadda muka fara da fitar da kayan sola zuwa Ghana.”

Ya bayyana cewa wannan mataki yana cikin shirye-shiryen gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Renewed Hope.

The Guradian ta rahoto ya ce shirin na mayar da hankali kan kirkire-kirkire, kera kaya masu inganci a cikin gida da dogaro da kai a tattalin arziki.

Ministan ya kara da cewa cigaban ya samo asali ne daga yarjejeniyoyin hadin gwiwa da aka kulla a wani taron makamashi da ya jawo masu saka jari daga cikin gida da waje.

Kara karanta wannan

Matatar Dangote za ta zama mafi girma a duniya, 'yan Najeriya za su samu ayyuka

Shirye-shiryen gwamnati a sashen lantarki

Ministan ya ce matakin na zuwa ne yayin da gwamnati ke aiwatar da sauye-sauye a sashen wutar lantarki, ciki har da sake fasalin TCN.

Ya ce ana shirin fadada karfin layin rarraba wuta, da kuma kaddamar da shirin samar da mita na kasa domin inganta raba wuta da jawo masu saka jari.

A cewar Adelabu, Najeriya ta riga ta tara sama da Dala biliyan 2 ta hanyar hadin gwiwa da bankin duniya, JICA, da NSIA.

Layin wutar lantarki
Ma'aikata na gyara a wani layin wutar lantarki. Hoto: Getty Images
Source: Facebook

Ya ce an yi haka ne domin tallafawa ayyukan samar da makamashi da wutar da ba ta karkashin kulawar gwamnati.

Najeriya za ta jagoranci bunkasa makamashi

Adelabu ya ce ƙarfafa masana’antar kera kayan makamashi a cikin gida zai taimaka wa Najeriya ta zama cibiyar samar da fasahar makamashi a yankin Afrika ta Yamma.

“Muna bude kofa ga duk wata hadin gwiwa da za ta taimakawa wajen saka jari da bunkasa wannan fanni,”

Kara karanta wannan

Majalisar dinkin duniya ta ce Najeriya ta zama abin koyi a kula da 'yan gudun hijira

- Inji shi.

An lalata layin wutar lantarki a Yobe

A wani rahoton, kun ji cewa wasu da ba a gano su waye ba sun lalata wani layin wutar gwamnatin tarayya a iyakar Gombe da Yobe.

Bayanin da hukumar TCN ta fitar ya nuna cewa lamarin ya jawo rashin wuta a jihohin Yobe da Borno.

Sai dai duk da haka, TCN ta bayyana cewa jami'anta sun dukufa da aiki wajen ganin an shawo kan matsalar cikin gaggawa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng