Aƙalla mutum uku sun mutu a cikin masallaci yayin da ‘yan bindiga suka kai hari ƙauyen Tsamaye a Sokoto, inda suka sace mutane tare da kwashe dabbobi da dukiyoyi.
Aƙalla mutum uku sun mutu a cikin masallaci yayin da ‘yan bindiga suka kai hari ƙauyen Tsamaye a Sokoto, inda suka sace mutane tare da kwashe dabbobi da dukiyoyi.
'Yan bindiga sun kashe Kanal Abdussalam Ude a birnin Abuja, yayin da matarsa, direbansa da jami'in tsaronsa suka jikkata. Ana ci gaba da bincike.
A ranar Alhamis, 10 ga watan Janairu, Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin sabuwar majalisar gudanarwa ta hukumar jin dadin Alhazai ta kasa (NAHCON).
An gano cewa dukiyar da zuriyar Sarkin Saudiyya suka mallaka ta ninka wacce attajiran duniya Musk da Gates suka tara. Zuriyar na da dalar Amurka tiriliyan 1.4.
Hukumar gudanarwa na bankin Musulunci na Ja'iz ya musanta jita-jitar cewa hukumar EFCC ta kama shugaban bankin Haruna Musa kan badakalar Betta Edu.
Dan Majalisar jihar Plateau, Hon. Adamu Aliyu ya bankado yadda ake korar Hausawa a yayin tantance masu neman aikin dan sanda a karamar hukumar Jos ta Arewa.
Madam Obebhatein Jonathan, yayar tsohon shugaban ƙasa, Dakta Goodluck Jonathan, ta riga mu gidan gaskiya bayan jinya a asibiti a Yenagoa, jihar Beyelsa.
Gwamnonin APC sun bukaci jama’a da su daina gaggawar yanke hukunci a kan ministar jin kai da aka dakatar har sai an tabbatar tana da laifi kamar yadda ake zargi.
Babbar kotun birnin tarayya Abuja ta amince da buƙatar belin tsohon ministan wutar lantarki, Olu Agunloye kan kudi Naira miliyan N50m, EFCC ce ta gurfanar da shi.
‘Yan bindiga sun sake yin garkuwa da wani malamin jami'ar tarayya da ke Gusau, jihar Zamfara, bayan da suka kutsa gidansa a safiyar ranar Laraba.
Tsohon mataimakin gwamnan jihar Legas, Femi Pedro, ya yi magana kan badƙaalar da dakatacciyar ministar jin kai da yaki da talauci, Betta Edu, ke ciki.
Labarai
Samu kari