Bayan Na Kano, Kotun Koli Ta Raba Gardama Kan Shari'ar Gwamnan PDP a Arewa, Ta Fadi Dalili

Bayan Na Kano, Kotun Koli Ta Raba Gardama Kan Shari'ar Gwamnan PDP a Arewa, Ta Fadi Dalili

  • Yayin da ake ci gaba da yanke hukuncin zaben gwamnoni a Abuja, Kotun Koli ta raba gardama a zaben jihar Plateau
  • Kotun ta tabbatar da Gwamna Caleb Mutfwang na jami'yyar PDP a matsayin halastaccen gwamnan jihar
  • Hausa Legit ta ji ta bakin wani dan jam'iyyar PDP kan wannan nasara ta Gwamna Caleb Muftwang

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Kotun Koli da ke birnin Tarayya Abuja ta yi hukunci kan zaben gwamna a jihar Plateau.

Kotun ta yi fatali da hukuncin Kotun Daukaka Kara da kuma ta sauraran kararrakin zaben gwamna a jihar.

Kotun Koli ta yi hukunci kan shari'ar zaben gwamnan jihar Plateau
Caleb Mutfwang ya yi nasara a Kotun Koli. Hoto: Nentawe Goshwe, Caleb Mutfwang.
Asali: Twitter

Wane hukunci kotun ta yanke a shari'ar Plateau?

Har ila yau, ta ayyana Gwamna Caleb Mutfwang a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar, cewar TVC News.

Kara karanta wannan

Kotun Koli ta yi hukunci kan shari'ar neman tsige gwamnan APC, bayanai sun fito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga bisani ta kori karar dan takarar gwamna a jam'iyyar APC, Nentawe Goshwe bayan samun nasara da ya yi a Kotun Daukaka Kara.

Hukumar INEC ta tabbatar da Caleb Mutfwang na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya yi nasara a zaben da aka gudanar a watan Maris.

Mene alkalin kotun ya ce kan shari'ar Plateau?

Yayin hukuncin kotun, Mai Shari'a, Emmanuel Agim ya ce dukkan kararrakin sun saba kaidar kotuna a kasar.

Agim ya kara da cewa matsalar jami'yya wani abu ne na cikin gida wanda Kotun Daukaka Kara ko wata daban ba ta da hurumi a kai.

Ya kara da cewa an dawo da mai kara da kuma tabbatar da zaben sa a matsayin gwamnan jihar, cewar Channels TV.

Legit Hausa ta ji ta bakin wani dan jam'iyyar PDP a Jos kan wannan nasara ta Gwamna Caleb:

Kara karanta wannan

Dauda Vs Matawalle: Kotun ƙoli ta bayyana sahihin wanda ya ci zaben gwamna a jihar Zamfara

Muhammad Sani Jos ya ce kamar yadda mu ka fada a baya muna da kwarin gwiwar yin nasara ganin yadda muka ta yin addu'a kan shari'ar.

Ya ce:

"Wannan nasara ce ta mutanen jihar ba iya 'yan PDP ba kadai, muna kira da a hada kai tun da yanzu komai ya kare na shari'a.
"Mun yi wa Allah godiya kan wannan nasara kamar yadda muka ta shi da azumi da addu'o'i."

Jami'yyar PDP ta koma ga Allah a jihar Plateau

A wani labarin, jami'yyar PDP a jihar Plateau ta roki magoya bayanta su tashi da shirin azumi da kuma addu'o'i.

Jami'yyar ta yi rokon ne a jiya Alhamis 11 ga watan Janairu kafin a yanke hukuncin Kotun Koli a yau Juma'a 12 ga watan Janairu.

A jiyan har ila yau, jami'yyar APC Mai adawa a jihar ta roki magoya bayanta su zama masu bin doka ganin yadda ake dakon hukuncin Kotun Koli.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel