Da Gaske Arzikin Zuriyar Sarkin Saudiyya Ya Ninka Na Elon Musk da Bill Gates? Gaskiya Ta Bayyana
- An gano cewa dukiyar da zuriyar Sarkin Saudiyya suka mallaka ta ninka wacce attajiran duniya Musk da Gates suka tara sau hudu
- Mujallar Forbes ta ruwaito cewa Elon Musk na da dukiyar da ta kai dalar Amurka biliyan 251.3 yayin da ta Bill Gates ta kai dala biliyan 119.6
- Sai dai an gano zuriyar Sarkin Saudiyyar, sun tara dukiyar da ta kai darajar dalar Amurka tiriliyan 1.4 kwatankwacin Euro tiriliyan 1.1
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
An yi ruwaito cewa zuriyar Sarkin Saudiyya mai mulki, sun mallaki dukiyar da ta kai kimar dalar Amurka tiriliyan 1.4 kwatankwacin Euro tiriliyan 1.1.
Hakan na nufin, ya ninka adadin dukiyar manyan attajirai biyu a duniya, Elon Musk da Bill idan aka hada su har sau hudu.
Arzikin da Musk da Gates suka mallaka
Mujallar Forbes ta kiyasta cewa Elon Musk, wanda ya kafa Tesla kuma mamallakin shafin X a halin yanzu yana da darajar dalar Amurka biliyan 241.6.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bill Gates kuwa a rahoton mujallar, wanda ya kafa Microsoft kuma mai ba da agaji, ya mallaki dukiyar da ta kai darajar dalar Amurka biliyan 119.9.
Gidan sarautar Saudiyya ya hada da zuriyar Muhammad bin Saud, wanda ya kafa masarautar Diriya a karni na 18, wanda kuma aka fi sani da kasar Saudiyya ta farko.
Yadda zuriyar Sarkin Saudiyya ta tara arzikin ta
Iyalin sun kunshi kusan mutum 15,000, kodayake yawancin dukiyar na hannun mutum kusan 2000 da ke a zuriyar, Daily Trust ta ruwaito.
Ana kyautata zaton arzikin da iyalin masarautar ya samo asali ne daga dimbin arzikin man da aka gano a kasar shekaru saba'in da suka gabata, a zamanin Sarki Abdulaziz ibn Saud.
‘Yan gidan masarautar Saudiyya suna boye bayanan kudadensu, amma salon rayuwarsu da makudan kudaden da suke kashewa galibi suna jan hankalin jama’a.
Rupert: Attajirin da ya doke Dangote a matsayin mai kudin Afrika
A wani labarin, shugaban kamfanin Compagnie Financiere Richemont, Mr Johann Rupert ya zama lamba daya a masu kudin Afrika.
Hakan na nufin Rupert ya zarce Aliko Dangote arziki, bayan Dangote ya shafe akalla shekaru 12 yana rike da kambun mafi yawan arziki a nahiyar Afirka.
Asali: Legit.ng