Masallacin Sultan Bello ya saki hotunan mutane da ya ce sun addabi jama'a da satar waya. An ce suna tafaka sata ne a lokacin da ake sallar Juma'a ko daurin aure.
Masallacin Sultan Bello ya saki hotunan mutane da ya ce sun addabi jama'a da satar waya. An ce suna tafaka sata ne a lokacin da ake sallar Juma'a ko daurin aure.
Shahararriyar jarumar finafinai a masana'antar Nollywood, Halima Abubakar, ta sauya addini daga Musulunci zuwa Kiristanci. Ta yi bayanin dalilin yin hakan.
Rundunar sojojin Najeriya ta yi magana kan kisan da aka yi wa sojoji a jihar Abia. Rundunar ta ce za ta mayar da martani mai zafi kan wannan mummunan danyen aikin.
Wata matar aure ta nemi a kashe aurenta sabida mijinta ya daina kwanciyar aure da ita bayan ya kara aure, ta ce kullum cikin ɓacin rai yake da neman faɗa da ita.
Yayin da jami'an tsaron Gwamnatin Tarayya ke gadin fadar Aminu Ado Bayero, ƴan tauri da ke gadin Sarki Muhammadu Sanusi II sun koka kan rashin ba su kulawa.
Jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta yabawa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, kan dawo da Muhammadu Sanusi II a kan sarautar Sarkin Kano.
Nadin mukaman da aka yi a jami’o’i da manyan makarantu ya bar baya da kura a kasar nan. A irinsu ABU za a koka a kan shugabannin da Tinubu ya zaba su sa mata ido.
Mun kawo wasu abubuwan da suka kunyata Bola Tinubu a shekarar farko. Da alama sabuwar gwamnatin Najeriya ta na da garaje, hakan yana jefa ta a matsala.
Sanata Rabiu Kwankwaso ya daura alhakin matsalolin da suka addabi yankin Arewacin Najeriya kan rashin adalci da kuma rashin kwarewa a shugabanci.
Wata kungiya ta taso Gwamna Abba Kabir Yusuf a gaba kan rikicin masarautar Kano. Kungiyar ta kawo mafita kan yadda za a warware rikicin masarautun.
Kotu ta ba da belin tsohon ɗan sanda, DCP Abba Kyari bayan shafe watanni 27 a gidan gyaran hali kan zargin alaka da manyan masu hada-hadar miyagun kwayoyi.
Labarai
Samu kari