Jarumar Fim Halima Abubakar Ta Sauya Addini daga Musulunci zuwa Kiristanci, Ta Fadi Dalili

Jarumar Fim Halima Abubakar Ta Sauya Addini daga Musulunci zuwa Kiristanci, Ta Fadi Dalili

  • Jaruma a babbar masana'antar fina-finai a Najeriya, Halima Abubakar ta sauya addini daga Musulunci zuwa Kiristanci
  • Halima Abubakar wadda ta yi suna a masana'antar fina-finai, ta bayyana cewa sauya addinin da ta yana da nasaba da warakar da ta samu
  • Jarumar ta bayyana cewa ta kwashe shekaru tana fama da rashin lafiya wanda ya jefa ta cikin mawuyacin hali da wahala

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Jarumar fina-finan Nollywood, Halima Abubakar, ta bayyana dalilin da ya sa ta yanke shawarar barin addinin Musulunci domin komawa addinin Kiristanci.

Halima Abubakar ta ce sauya addinin ta ya biyo bayan abin da ta bayyana a matsayin samun waraka ta mu'ujiza daga wata cutar asiri da ta sa ta kwashe kusan shekaru tara a kwance.

Halima Abubakar ta fice daga addinin Musulunci
Jaruma Halima Abubakar ta masana'antar Nollywood Hoto: Nollywoodcitadel
Source: Instagram

Jarumar ta bayyana cewa shekaru da dama tana fama da rashin lafiyar tare da tsallake rijiya da baya a lokuta da dama, rahoton jaridar Tribune ya nuna hakan.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya nuna damuwa kan gargadin da Majalisar ɗinkin duniya ta yi wa Arewacin Najeriya

Halima Abubakar ta godewa Ubangiji

Halima Abubakar ta ce ta gamsu cewa Ubangiji Ya ba ta dama ta biyu ta rayuwa, wanda hakan ya zaburar da ita wajen sadaukar da kanta don bauta ga Yesu Almasihu.

A cewar Halima, farfadowarta ba kawai komawa ga koshin lafiya ba ne, a'a, wani sauyi ne wanda ya gamsar da ita ta bayyana sabon addininta a fili kuma ta fadi abin da ya faru ga sauran mutane, jaridar The Sun ta kawo labarin.

Meyasa ta koma Kiristanci?

"Ni sabuwar mutum ce yanzu. Na ba da rayuwata ga Almasihu. Ina so na bawa Allah gaskiya domin Ya taimake ni. Na kusan mutuwa. Sun kusan kashe ni. Wannan ba batun fina-finai ba ne; wannan magana ce ta mayar da abin da aka rasa da kuma shaida. Halima Abubakar ta dawo, cikin karfi da kwarin gwiwa."
"A yanzu haka, a shirye nake na bawa Ubangiji gaskiya domin Yana so na yi hakan. Ya cece ni, saboda haka ina bukatar in bauta Masa kuma na yi wa mutane wa'azin bishararsa."

Kara karanta wannan

Kwankwasiyya ta shiga batun ma'aikatar bogi, ta aika sako ga gwamnatin Tinubu

- Halima Abubakar

Ta shirya yin bayani

Halima ta kuma bayyana cewa nan ba da dadewa ba za ta bayar da shaida a fili da ke bayyana dalla-dalla yadda, a cewarta, Ubangiji Ya taimake ta, ta hanyar cocim Queen Belemzy Ministries (School of Power) don dawo mata da lafiyarta bayan shekaru na wahala.

A farkon wannan shekarar, jarumar ta bayyana cewa mai gidan da take hayar gidanta ta umarce ta da ta tashi daga gidan duk da cewa tana da shirin sabunta hayarta.

Halima Abubakar ta koma addinin Kiristanci
Jaruma a masana'antar Nollywood, Halima Abubakar Hoto: Nollywoodcitadel
Source: Instagram

Ta kuma bayyana cewa har yanzu tana karbar magani, wanda hakan ke nuna irin nauyin bacin rai da na kudi da rashin lafiyar tata mai tsawo ta janyo mata.

Tare da sabon bayyanawar tata, Halima ta ce tana barin shekaru na zafi da rashin tabbas a baya yayin da take shiga abin da ta bayyana a matsayin sabuwar rayuwa ta imani, waraka, da mayar da abin da aka rasa.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Kotu ta ƙwace Naira miliyan 150 na wani 'dan Majalisar tarayya a Najeriya

Jarumin fim ya rasu

A wani labarin kuma, kun ji cewa masana’antar fina-finan Nollywood ta yi rashin fitaccen ɗan wasa, marubucin wasan kwaikwayo mai suna Kola Oyewo.

Kafin rasuwarsa, Oyewo ya bayyana matsalolin lafiyarsa a wani bidiyo da ya yi tare da jarumi Kunle Afod a shekarar 2024.

Fitaccen jarumin, wanda ya rasa matarsa a shekarar 2020, ya bayyana yadda likitoci suka sanar da shi cewa yana fama da kumburin mafitsara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng