An Saki Hoton Barayin Waya Masu Sata a Masallacin Sultan Bello

An Saki Hoton Barayin Waya Masu Sata a Masallacin Sultan Bello

  • Hukumomin masallacin Juma'a na Sultan Bello da ke Kaduna sun kama wasu mutanen da ake zargi suna tafka sata a lokacin da ake sallah
  • Rahotannin sun tabbatar da cewa ana zargin wadanda aka kaman ne da satar wayoyin mutane a lokacin da suka shagala da ibada a masallacin
  • Sanarwar da masallacin ya fitar ta nuna cewa an fi tafka satar wayoyin hannu ne a lokutan da ake sallar Juma'a ko lokutan da ake daurin aure

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Shugabannin masallacin Sultan Bello da ke jihar Kaduna sun yi nasarar cafke wasu da ake zargi sun addabe su da sata.

Masallacin ya sanar da cewa ya cafke wasu matasa da ake zargi su suka dauki tsawon lokaci suna satar wayoyin jama'a a lokutan ibada.

Kara karanta wannan

An rike dan ta'adda da ya nufi fadar sarki da bindiga zai kai hari

Barayin waya a masallaci
Wadanda ake zargi da satar waya a Sultan Bello da ke Kaduna. Hoto: Sultan Bello Mosque, Kaduna.
Source: Facebook

Legit Hausa ta tattaro sako game da kama wadanda ake zargi da satar ne a wani bayani da masallacin Sultan Bello ya wallafa a shafinsa na Facebook.

An kama barayin waya a masallaci

Sanarwar kama wadanda ake zargi da satar wayoyin hannu a masallacin Sultan Bello ta nuna cewa mutane uku aka cafke cikin wadanda ake zargi.

Sanarwar ta ce:

"Barayin wayoyin masallata a masallacin Sultan Bello da ke Kaduna, sun addabi jama'ah wurin dauke masu waya musamman lokacin sallar Juma'ah da daure-dauren Aure.
'Jiya dubunsu ta cika."

Bayan tabbatar da kama mutanen, masallacin Sultan Bello ya yi addu'a da cewa:

"Muna rokon Allah hakan yasa sanadiyar shiriyar su ne kuma izina ga 'yan baya masu matattun zuciya."

Martanin jama'a kan kama barayin

Mutane da dama sun tsokaci game da barayin da aka kama, inda Rabi'u Sa'idu Baita ya ce:

"Allah ya shirye su da Musulmi baki daya, amma bayyanar da fuskokinsu ya kamata a gyara, bai kamata ba gaskiya.

Kara karanta wannan

Yadda dannau ya danne 'yan bindiga a barci, wadanda suka sace suka gudu

"Hotonsu ajiye shi ya kamata a yi a cikin fayal na masallaci saboda gaba ba wai a bude hotonsu ba, masallaci wurin wa'azine da rufama musulmi asiri bawai bayyanar da aika-aikan musulmi ba saboda kowa yana son Allah ya rufa mai asirin shi duniya da kiyama. Allah yasa mu dace."
Masallacin Sultan Bello a Kaduna
Masu ibada a masallacin Sultan Bello. Hoto: Sultan Bello Mosque, Kaduna
Source: Facebook

BM Jidda ma ya soki yadda aka wallafa hotunan mutanen da cewa:

"Ban ga amfanin ɗaura hotuna idan mutum ya yi laifi ba, idan Allah ya shiryi mutum to Allah yakan goge masa zunuban sa ko da a filin alkiyama ba za a bijiro da zancen ba, amma idan ka daura mutum a midiya ta yaya za a yi ka goge wannan bayan shiryar Allah ta zo masa alhalin kai baka sani ba?
"Shi Allah ya shirye shi ya yafe masa kai kuma hoton yana nan a midiya, kai ya sunan ka kenan?
"Allah ya ƙara mana shiriya, ya shiryar da ɓatattun cikin mu."

Mahee Abubakar Smart ya ce:

"Allah ka shirye su.
"Allah ya kara ba mu cikakken zaman lafiya a kasar mu baki daya. Amin."

Salisu Usman ya goyi bayan saka hotunan su yana cewa:

"Ku da kuka ce daura hotunan su bai dace ba, da abin yabo suka aikata sai a ce shi ma nuna hotonsu bai dace ba.

Kara karanta wannan

Uba Sani: 'Yan sanda sun kama mutum 100 kan kisan Ummulkhairi a Kaduna'

"Dama ba a ranar suka fara ba, asirinsu ne ya tonu don an ce gani ga wane ya ishi wane tsoron Allah."

Ana rikici kan mallakar masallatai

A wani labarin, kun ji cewa jagoran Darikar Tijjaniyya, Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi ya bukaci a ware masu masallatai a jami'o'in Najeriya.

Ya bayyana cewa ba za su yarda wanda ba dan akidarsu ya jagorance su ba sam, inda ya ce samar masu da masallatai ne zaman lafiya.

Malamin ya yi magana ne bayan wani rikicin da ya taso a jami'ar ATBU da ke Bauchi kan ba 'yan Darikar Tijjaniyya masallacin da suka kebanta da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng