'Dan Gwamna Ya Tada Kura da Ya Saki Bidiyo Yana Rera Wakar Sukar Tinubu da Mahaifinsa
- 'Dan gwamnan jihar Anambra, Ozonna Soludo ya haddasa ce-ce-ku-ce bayan ya wallafa bidiyo yana rera wakar da aka soki Shugaba Bola Tinubu
- A faifan bidiyon, an ga dan gwamnan yana tika rawa a wakar da aka soki Tinubu, mahaifinsa da wasu fitattun yan siyasa a Najeriya
- Ozonna mawaki ne, mai ƙirƙirar bidiyo da kuma mai tasiri a kafafen sada zumunta, inda ya shahara wajen wallafa bidiyoyin rawa da salon rayuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Anambra, Nigeria - Ozonna Soludo, ɗan gwamnan Jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo, ya tayar da ƙura sakamakon wani bidiyo da ya wallafa a shafukan sada zumunta.
A faifan bidiyon, an ga ɗan gwamnan yana rawa tare da rera wata shahararriyar waka da ke sukar wasu fitattun 'yan siyasar Najeriya, ciki har da mahaifinsa, Gwamna Soludo.

Kara karanta wannan
Hadimin Abba ya nanata zargin da ake yi wa Abdusalam Gwarzo na yin kwana da N308m

Source: Facebook
Dan gwamna ya tada ƙura a bidiyo
Ozonna Soludo ya wallafa wannan bidiyo ne a shafinsa na Facebook, lamarin da ya jawo hankalin jama'a.
An ga ɗan gwamnan yana rera wakar tare da rawa yayin da wakar ta fara da kalmomin:
"Tinubu, ka ji kunya, mulki na Ubangiji ne."
Bayan haka, wakar ta ambaci Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima; Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio; Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike; da Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma.
Yadda wakar ta soki Gwamna Soludo
Sauran 'yan siyasar da aka ambata a cikin wakar sun hada da Gwamnan Jihar Enugu, Peter Mbah; tsohon hadimin shugaban kasa, Reno Omokri; Ministan Ayyuka, David Umahi; da tsohon Sanatan Kogi ta Yamma, Dino Melaye.
Sai dai lokacin da wakar ta kai inda aka ce, "Soludo, ka ji kunya," Ozonna ya dan kada idanu, amma bai tsaya ba, ya ci gaba da rawa tare da rera wakar.

Kara karanta wannan
DSS da yan sanda sun yi bincike, an ji gaskiya kan ɓullar sabuwar ƙungiyar ta'addanci a Najeriya
Cikin kankanin lokaci, bidiyon ya bazu sosai a shafukan sada zumunta, inda ya samu sama da tsokaci 3,000 daga masu amfani da kafafen.
Mutane da dama sun yi martani kan yadda dan gwamnan ya shiga wannan salo duk da cewa wakar ta soki mahaifinsa kai tsaye.

Source: Twitter
Ozonna ya saba jawo ce-ce-ku-ce
Wannan bidiyo ya shiga jerin abubuwan da suka sa Ozonna ke yawan zama abin tattaunawa saboda salon rayuwarsa da abubuwan da yake wallafawa a kafafen sada zumunta.
Ozonna mawaki ne, mai kirkirar bidiyo da kuma mai tasiri a kafafen sada zumunta, inda ya shahara wajen wallafa bidiyoyin rawa da salon rayuwa, lamarin da ke haifar da ra'ayoyi mabambanta, cewar rahoton Daily Trust.
A watannin baya, ya jawo ce-ce-ku-ce bayan ya bayyana sabon salon kitso a gashin kansa, inda ya ce ba zai sauya kamanninsa ba saboda sukar da ake yi masa.
Gwamna Soludo ya goyi bayan Tinubu
Kun ji cewa gwamnan jihar Anambra, Chukwuma Soludo ya nuna goyon bayansa ga tazarcen shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaben shekarar 2027.
Soludo ya jaddada cewa dole ne yan kabilar Ndigbo da je d rinjaye a jihar Anmbra da Kudu maso Gabashin Najeriya, su guji ɓata ƙuri'unsu a zaɓubbuka masu zuwa.
Gwamnan ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya samu nasara a zaben 2023 duk da cewa yankin Kudu maso Gabas bai ba shi kuri'u ba.
Asali: Legit.ng
