"Bai Kamata Suna Samun Kason Gwamnati Ba", Ministan Buhari Ya Tsame Kano Kan Haramta Giya

"Bai Kamata Suna Samun Kason Gwamnati Ba", Ministan Buhari Ya Tsame Kano Kan Haramta Giya

  • Tsohon Ministan lafiya a Najeriya, Isaac Adewole ya koka kan rarraba kudin kasar da wasu jihohi da suka haramta giya
  • Adewole ya ce bai kamata a raba kudin giya na Najeriya da jihohin da suka haramta siyar da giya ba a halin da ake ciki
  • Tsohon Ministan ya bayyana haka ne a jiya Juma'a 31 ga watan Mayu yayin hira da gidan talabijin na Channels

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohon Ministan lafiya, Farfesa Isaac Adewole ya magantu kan tsarin rarraba arzikin kasa ga jihohi.

Adewole ya ce ya kamata a saka doka kan duka jihohin da suke haramta siyar da giya a jihohinsu wurin rarraba kudin shiga na Gwamnatin Tarayya.

Kara karanta wannan

"Shugaba Tinubu ya saba doka", Kungiyar lauyoyi za ta kotu saboda an sauya taken Najeriya

Ministan Buhari ya magantu kan jihohi da suka haramta giya kamar Kano
Tsohon Ministan lafiya, Isaac Adewole ya magantu kan rarraba arzikin Najeriya. Hoto: Isaac Folorunso Adewole.
Asali: Facebook

Ministan ya bukaci hana wasu jihohi kaso

Tsohon ministan ya ce duka jihohin da suka haramta giya bai kamata suna samun kaso na kuɗin giya daga Gwamnatin Tarayya ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Farfesan ya bayyana haka ne a jiya Juma'a 31 ga watan Mayu yayin hira da gidan talabijin na Channels.

"Ya kamata mu yi duba zuwa ga yadda ake rarraba kudi na Gwamnatin Tarayya ga jihohi."
"Idan akwai doka a jiha na haramta siyar da giya, bai kamata jihar ta samu kaso daga kudin giya da ake rabawa ba."
"Ya kamata mu fadawa kan mu gaskiya rashin adalci ne raba kudin kasa daga giya ga wadanda suka haramta giya a jihohinsu."

- Isaac Adewole

A bayyane yake, jihar Kano ta haramta siyarwa da sha da kuma safarar giya a fadin jihar domin rage badala.

Kara karanta wannan

Taken Najeriya: Tinubu ya yi karin haske kan hikimar komawa tsohon taken kasa

Minista ya koka kan dogaro da mai

Ministan har Ila yau, ya bukaci faɗaɗa hanyoyin samun kudin shiga a Najeriya inda ya koka kan dogaro da mai.

Ya ce abin takaici ne yadda jihohi suka dogara da kudin mai a Najeriya inda ya ce shi ya tsayar da kasar a wuri daya.

Adewole ya ce wasu jihohi da dama ba su iya kawo wani gudunmawa na ci gaban ƙasa musamman ta fannin tattalin arziki.

Kwankwaso ya magantu kan matsalolin Arewa

A wani labarin, kun ji cewa Sanata Rabiu Kwankwaso ya bayyana musabbabin matsalolin Arewacin Najeriya.

Kwankwaso ya ce rashin iya shugabanci da kuma tsantsar rashin adalci su ne manyan matsalolin da ke damun yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.