Babu wani abin da ke nuna Abduljabbar Kabara ya tuba a sababbin jawabansa inji Baba Impossible

Babu wani abin da ke nuna Abduljabbar Kabara ya tuba a sababbin jawabansa inji Baba Impossible

  • Gwamnatin Kano ba ta gamsu da ‘tubar’ da Abduljabbar Nasiru Kabara ya yi ba
  • Dr. Muhammad Tahar Adam yace jawaban Malamin da ke yawo ba su nuna tuba ba
  • Kwamishinan yace akwai sharudan tuba a musulunci, wanda Shehin bai bi su ba

A wani faifen murya da ya shigo hannun Legit.ng, kwamishinan harkokin addini a Kano, ya yi magana a kan tubar da ake cewa Abduljabbar Nasiru Kabara ya yi.

A baya an rahoto Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya na cewa ya tuba, har ya nemi afuwar jama’a.

Dr. Muhammad Tahar Adam wanda aka fi sani da Baba Impossible ya nuna cewa babu wani wuri da shehin malamin ya ayyana cewa lallai ya tuba daga kuskurensa.

KU KARANTA: Ba a fahimce ni bane inji Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara

Mai girma kwamishinan harkokin addinin na jihar Kano ya ce Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya ce ya janye kalamansa ne, wanda hakan bai nufin neman gafara.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta soke kwangilar jirgin kasan Fatakwal zuwa Maiduguri inji Amaechi

“Idan aka dubi abin, za a ji cewa ya yi, ya janye, to ba a gane abin da ya janyen ba.”
“A musulunci sharadin tuba uku ne; mutum ya yi nadama a kana bin da ya aikata, sannan ya yi niyyar ba zai kara yi, kuma idan ya na cikin yin (laifi), ya janye.”
“Babu inda ya ce ya yi kuskure a cikin maganarsa, kuma abin da aka nema kenan. Wannan abin da ya yi kuskure ne. Sai ya ce ya yi kuskure, sannan za a ce ya tuba.”

KU KARANTA: Na janye kalamaina - Abduljabbar Kabara

Abduljabbar Kabara
Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara Hoto: www.dw.com/ha
Asali: UGC
“Don haka babu inda ya tuba. Sannan abu na biyu, a kan zagin Annabi Muhammad (SAW), ba a tuba, domin babu mai ikon yafe hakkin Manzon Allah (SAW).”

Kwamishinan ya kara da cewa malamai ya kamata a samu, suyi cikakken bayani a kan abin da addinin musulunci ya ce game da mas’alar taba Ma’aikin Allah SWT.

Kara karanta wannan

Bayan shekaru biyu da zabe, Buhari ya bayyana abin da ya sa APC ta rasa wasu jihohi a 2019

Muhammad Tahar Adam ya ce a bangarensu, za su rubuta rahoto da za a kai wa gwamnatin Abdullahi Ganduje domin ta dauki matakin da ya dace da malamin.

Kwamishinan ya gargadi masu shirin tada rigima a Kano da su guji yin abin da ya saba wa doka.

A baya mun tattaro maku jerin muhimman abubuwa da su ka wakana tsakanin Abduljabbar Kabara da Malaman Ahlus Sunnah a muqabalar da su ka yi a Kano.

Sheikh Abduljabbar Kabara bai iya bada amsoshin da aka yi masa ba, ya ce lokacin da aka ware ya yi masa kadan. An shafe sa'o'i hudu ana yin wannan tattauna wa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng