Ba za mu taba barin Jihar Anambra ba - Hausawa mazauna Kudu ga NEF

Ba za mu taba barin Jihar Anambra ba - Hausawa mazauna Kudu ga NEF

- Hausawa mazauna jihar Anambra sun ce ba za su bar jihar ba

- Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta fadawa makiyaya su bar yankunan kudancin kasar saboda barazanar da aka yi wa rayuwarsu

- Amma sakataren kungiyar Hausawa na garin Nnewi, Sani Suleiman ya ce da wuya su bar kudancin Najeriya bayan sun shafe shekaru kusan arba'in a yankin

Hausawa mazauna garin Nnewi da ke jihar Anambra sun ce ba su da niyyar barin jihar bayan umurin da kungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta bayar na cewa su bar yankin saboda rayuwarsu na cikin hatsari.

Vanguard ta ruwaito cewa mambobin kungiyar ta Dattawan Arewa NEF da Kungiyar hadakar kungiyoyin Arewa sun bukaci Fulani makiyaya su bar kudancin kasar saboda ikirarin da su kayi na cewa rayuwarsu na cikin hatsari.

DUBA WANNAN: Dalilin da ya sa Arewa ke hakuri da Buhari - Shehu Sani

Legit.ng ta gano cewa sakataren kungiyar Hausawa mazauna Nnewi, Sani Suleiman za yi wahala su bar kudancin Najeriya duba da cewa sun shafe fiye shekaru 30 suna zaune lafiya da mazauna yankin.

A cewarsa, wasu daga cikin su sun shafe fiye shekaru 40 a yankin saboda haka duk wanda ke cewa suyi hijira daga yankin ya yi kuskure.

Ya ce: "Wasu daga cikin mu sun suna zaune a kudu tun 1986 saboda haka ba zi yi wu wani ya zo rana tsaka ya ce mu koma jihohin da muka fito ba.

"Allah da ya hallici Najeriya ya hada mu wuri daya ya fi mu sanin dalilin sa na yin hakan. Mutum daya ba zai farka ya raba kan mu saboda son zuciyarsa ba. Kamar yadda muke zama lafiya a nan Nnewi akwai wasu kabilun da ke zamansu a Arewa kuma babu yadda za ayi wani ya ce su koma yankunnan su. Ba zai yi wu ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel