INEC ta yi barazanar dakatar da zaben gwamna a jihar Edo

INEC ta yi barazanar dakatar da zaben gwamna a jihar Edo

- Hukumar zabe INEC ta kasa (INEC) ta ce ba zata yi sanya wajen dakatar da shirin gudanar da zaben gwamna ba a jihar Edo

- INEC ta ce za ta dakatar da zaben ne matukar jam'iyyun siyasa da 'yan takarar da zasu fafata a zaben ba su yi riko da matakan tabbatar da zaman lafiya ba

- Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya nuna takaicinsa bisa gazawar hukumar wajen hukunta ma su aikata laifukan zabe

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta yi barazanar cewa za ta dakatar da shirye - shiryen gudanar da zaben kujerar gwamna a jihar Edo matukar za a samu hatsaniya da tashin hankali.

INEC ta gagargadi jam'iyyun siyasa da 'yan takarar da za su fafata a zaben na ranar 19 ga watan Satumba da kada su kuskura su kawo tashin hankali ko kuma rashin zaman lafiya ta kowacce irin siga.

Kwamishina mai kula da harkar yada labarai da ilimantar da ma su kada kuri'a, Festus Okoye, ne ya sanar da hakan yayin da ya ke magana lokacin da ake gudanar da wani shiri a kan gyaran harkar zabe wanda aka nuna kai tsaye a gidan talabijin din 'Channels'.

INEC ta yi barazanar dakatar da zaben gwamna a jihar Edo
Shugaban INEC; Farfesa Mahmood Yakubu
Asali: Original

A cewarsa, hukumar INEC ba za ta yi wasa da kula da tsaron lafiyar ma'aikatanta da sauran ma'aikatan da za su yi aiki yayin zaben ba.

DUBA WANNAN: Hukumar NIS ta yi karin bayani a kan hanyar daukan aiki, ta garagadi ma su nema

"Kar 'yan siyasa su gwada hakurinmu, za mu dakatar da dukkan wani shirin gudanar zabe idan akwai barazanar samun tashin hankali.

"Mu na aiki da ma'aikatan wasu hukumomin gwamnatin tarayya lokutan zabe, ba za mu so a kashe wani mutum yayin da ya ke yi ma na aikin wucin gadi ba," a cewarsa.

Kazalika, shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya nuna takaicinsa a kan gazawar INEC wajen hukunta ma su aikata laifuka yayin gudanar da zabe.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel