Wani dan takarar shugaban kasa ya roki 'yan Najeriya Naira miliyan 3.5 na siyen fom din takara

Wani dan takarar shugaban kasa ya roki 'yan Najeriya Naira miliyan 3.5 na siyen fom din takara

- Wani dan takarar shugaban kasa ya roki 'yan Najeriya Naira miliyan 3.5 na siyen fom din takara

- Yace shi bai da su kuma yana so yayi takarar

- Ya bukaci 'yan Najeriya su sadaukar da dukiyar su don kawo cigaban kasa

Daya daga cikin 'yan takarkarin kujerar shugaban kasar Najeriya a zabukan 2019 dake tafe mai suna Fela Durotoye, ya roki 'yan kasar da su taimaka masa su tattara masa kudin da zai sayi fom domin takarar tasa a jam'iyyar adawa ta Alliance for a New Nigeria (ANN).

Wani dan takarar shugaban kasa ya roki 'yan Najeriya Naira miliyan 3.5 na siyen fom din takara
Wani dan takarar shugaban kasa ya roki 'yan Najeriya Naira miliyan 3.5 na siyen fom din takara
Asali: Instagram

KU KARANTA: Buhari yayiwa manyan kasar Najeriya tatas

Mun samu cewa fom din takarar shugabancin kasar na jam'iyyar adawar dai ana saida shi ne akan Naira miliyan 3.5 wanda ya bayar da shawarar cewa da an samu mutane kadan da kowa ya bayar da Naira dubu daya to za a hada masa kudaden fom din.

Legit.ng ta samu haka zalika cewa Mista Fela Durotoye ya kara da cewa dole ne 'yan Najeriya sai sun sadaukar da wani bangare na dukiar su da jin dadin su ne kadai sannan za su iya tabbatar da shugabanci na adalci.

A wani labarin kuma, Shugaban kasar Najeriya Muhammadu ya nuna rashin jin dadin sa game da yadda yace wadanda ke kiran kan su manya a Najeriya suka yi shiru shekaru 16 lokacin da jam'iyyar PDP ke mulkin kasa duk kuwa da yadda suka lalata kasar.

Ya kara da cewa hakan haka zalika abun takaici ne yadda kuma yanzu wasun su ke ta kumfan baki suna cewa wai baya da sauri bayan duka-duka shekaru 3 kadai yayi yana mulki.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel