Hotunan da suka lashe gasar kyawawan hotuna ta duniya a wannan shekarar
Wannan hoto an dauke shi ne a kauyen Upernavik inda ake kiwon kifi a yankin tsibirin Greenland, hoton ya baiwa wanda ya daukeshi damar lashe gasar kyawawan hotuna na duniya wanda matafiya suke dauka

Asali: Facebook
Wanda ya dauki hoton mai suna Mista Chu, ya cinye sama da shekara daya yana kai ziyara yankin Greenland kafin daga baya ya yanke shawarar daukar hoton yanayin rayuwar mutanen tsibirin, inda kuma ya fara daukar hoton nashi daga Kauyen Upernavik.
Ga sauran mutanen da suka samu nasara a gasar, da kuma takaitaccen bayani akan hotunansu:
Hoton birni na biyu - daga Jassen Todorov

Asali: Facebook
"Akwai tituna na tashi da saukar jiragen sama a filin jirgin San Francisco dake kasar Amurka. Nayi kokarin daukar hoton filin jirgin a lokacin da nake cikin jirgin sama.
"Sai dai kuma anyi wata irin iska a lokacin wacce gudunta ya kai kimanin mil 35 zuwa 45 a kowacce sa'a, inda sanadiyyar hakan yasa jirgin ya ringa yin rawa a sararin samaniya, hakan yasa na sha wahala wurin daukar hoton," in ji Jassen Todorov.
Hoton birni na uku - Daga Sandipani Chattopadhyay

Asali: Facebook
"Mutane na gabatar da sallah akan titin birnin Dhaka na kasar Bangladesh, a lokacin bikin addinin Ijtema. Bishwa Ijtema yana daya daga cikin manyan bukukuwan addinin Musulunci wanda ake yi kowacce shekara a birnin Dhaka, miliyoyin al'ummar musulmi ne ke halartar wannan sallah a kasar.
"Am ware wani katon fili ne domin gabatar da sallah a kasar, duk da katon filin da aka ware mutane da yawa basa samun wurin gabatar da sallar, hakan ya sanya wasu yin sahu akan tituna," in ji Sandipani Chattopadhyay.
Hoton mutane na daya - Daga Huaifeng Li

Asali: Facebook
"An dauki hoton ne a lokacin da 'yan film ke shirin yin wasa a garin Licheng na kasar China. na shafe kusan kwanaki uku ina tare da 'yan film din tun daga lokacin kwalliyarsu har zuwa lokacin da aka fara haska fim din."
Hoton mutane na biyu - Daga Yoshiki Fujiwara

Asali: Facebook
"Wannan hoto an dauke shi a wani wurin shakatawa a birnin Hong Kong. A lokacin da na je ziyara da yammacin ranar da zan dauki hoton, wurin ya cika da matasa suna ta daukar hotuna sannan wasu na can na buga kwallon kwando."
Hoton halittu na daya - Tamara Blazquez Haik

Asali: Facebook
"Wannan hoton wata ungulu ce da aka dauki hoton ta a daidai lokacin da take shawagi a sararin samaniyar wani katon daji da ake kira dajin Monfrague National Park dake kasar Spaniya."
Hoton hallitu na biyu - Daga Danny Sepkowski

Asali: Facebook
"Wane abu ne zai faru kafin igiyar ruwa ta tsinke? Wannan tambaya tana daya daga cikin tambayoyin dana sanya a raina a shekarar da ta gabata. Tun daga wannan rana na kudiri aniyar daukar hoton yadda rana ke faduwa a garin Oahu na jihar Hawaii dake kasar Amurka," in ji Danny Sepkowski.
Hoton hallittu na uku - Daga Scott Portelli

Asali: Facebook
"Wannan wani nau'in kifi ne wanda baya tafiya shi daya dole sai tare da ayari a gabar tekun Kaikoura dake kasar New Zealand domin ya samu abincin ci," in ji Scott Portelli.
Hoton halittu na hudu - Daga Jonas Schafer

Asali: Facebook
An dauki hoton wadannan dabobbi a kasar Switzerland a lokacin da suke shirin tsallaka wata gabar kogi ta tafkin Brienz.
Hotuna daga National Geographic Travel Photo Contest 2019.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng