Babban Dan Siyasa Ya Yi Hadarin Mota Ya Rasu ana Shirin 2027
- Shugaban Majalisar Dokokin jihar Bauchi, Abubakar Y. Suleiman, ya yi jimamin rasuwar shugaban ƙaramar hukumar Zaki, Hon. Mas'ud Aliyu Umar
- Marigayin ya rasu ne a yammacin ranar Lahadi sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da shi a ƙauyen Konkiyel, bayan halartar taron APM
- Shugaban majalisar ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga iyalansa, al'ummar Zaki da jihar Bauchi baki ɗaya, yana mai yabawa marigayin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Bauchi – Shugaban Majalisar Dokokin jihar Bauchi, Rt. Hon. Abubakar Y. Suleiman, ya yi jimamin rasuwar shugaban ƙaramar hukumar Zaki, Hon. Mas'ud Aliyu Umar.
Marigayin ya rasu ne a yammacin ranar Lahadi a wani hatsarin mota da ya faru a ƙauyen Konkiyel, bayan halartar taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APM a babban birnin jihar.

Source: Facebook
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban majalisar, Mukhtar Garba Kobi, ya fitar a Facebook a ranar 2 ga Nuwamba, Abubakar ya miƙa ta'aziyyarsa ga iyalan mamacin da al'ummar ƙaramar hukumar Zaki.
Halayen marigayi Hon. Aliyu
Shugaban majalisar ya bayyana cewa rasuwar Hon. Mas'ud Aliyu Umar babban rashi ne ba ga iyalansa kaɗai ba, har ma da al'ummar Zaki da jihar Bauchi baki ɗaya.
Ya bayyana marigayin a matsayin shugaba mai jajircewa, sadaukarwa da tausayi, wanda ya gudanar da ayyukansa cikin gaskiya da kishin al'umma.
Abubakar ya ce marigayin ya taka muhimmiyar rawa wajen taimakon jama'a tun kafin ya zama shugaban ƙaramar hukumar Zaki, musamman lokacin da yake matsayin Darakta Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta jihar Bauchi (SEMA).
Gudummawar marigayin
Shugaban majalisar ya ce lokacin da marigayin yake jagorantar hukumar SEMA, ya taimaka wa mutanen da ibtila'in bala'o'i ya shafa, ta hanyar samar musu da kayayyakin agaji da sauran tallafin jin ƙai.
Ya ƙara da cewa gudummawar da marigayin ya bayar wajen inganta rayuwar jama'a, kasuwancin cikin gida da ci gaban al'ummomi za ta ci gaba da kasancewa abin tunawa.
Ya bayyana cewa marigayin ya taimaka wajen rage wa mabukata wahala, farfaɗo da iyalan da bala'o'i suka shafa tare da gaggauta kai musu tallafin da suke buƙata.
Abubakar ya ce irin salon jagoranci da tasirin da marigayin ya yi a rayuwar al'umma ya kamata sauran shugabanni su yi koyi da shi.

Source: Original
A madadin kansa, mambobin majalisar da ma'aikatanta, shugaban majalisar ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta wa marigayin tare da sanya shi cikin Aljannatul Firdausi.
Ciyaman ya rasu a Adamawa
A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban ƙaramar hukumar Fufore ta jihar Adamawa, Yahaya Saidu, ya rasu a wani asibiti da ke Kaduna, ƙasa da wata uku bayan hawansa muƙamin.
Ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomi ta Najeriya (ALGON) reshen jihar Adamawa ce ta sanar da rasuwarsa, inda ta bayyana mutuwar a matsayin babban rashi ga iyalansa da al'ummar jihar.
Shugaban ALGON na jihar, Titus Obadiah, ya bayyana marigayin a matsayin shugaba mai kishin jama'a da ya sadaukar da kansa wajen yi musu hidima.
Asali: Legit.ng

