Biliyoyin Bashi a Bangaren Lantarki da ke Barazana ga Samar da Wuta a Najeriya

Biliyoyin Bashi a Bangaren Lantarki da ke Barazana ga Samar da Wuta a Najeriya

  • Masu ruwa da tsaki a bangaren wutar lantarki sun yi gargadi kan bashin sama da Naira biliyan 639 da ake bin masu samar da iskar gas
  • Wani jami'in NNPC ya ce kamfanonin samar da wutar lantarki ba sa samun isassun kuɗaɗen biyan kuɗin iskar gas
  • Masana sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta samar da ingantaccen tsarin biyan kuɗi tare da ƙara zuba jari wajen samar da iskar gas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja – Masu ruwa da tsaki a bangaren wutar lantarki sun yi gargaɗin cewa matsalar basussukan da ake bin masu samar da iskar gas na iya ƙara ta'azzara matsalar rashin wutar lantarki a Najeriya.

Sun ce bashin da ya haura Naira biliyan 639, ƙarancin zuba jari wajen samar da iskar gas da kuma rashin ingantattun kayan aikin lantarki na daga cikin manyan abubuwan da ke kawo cikas ga samar da wutar lantarki mai ɗorewa.

Kara karanta wannan

Hatsabibin ɗan bindiga da ya addabi jama'a ya sheƙa barzahu a Katsina

Bashin gas na barazana ga wutar lantarki a Najeriya
Ministan makamashi a Najeriya, Joseph Tegbe. Hoto: Federal Ministry of Power.
Source: UGC

Masana sun bayyana hakan ne a taron shekara-shekara karo na shida na ƙungiyar 'yan jaridun da ke kula da harkokin wutar lantarki a Najeriya, wanda aka gudanar a Abuja, cewar Punch.

Sun yi gargaɗin cewa idan ba a magance matsalolin kuɗaɗe da tsarin gudanar da bangaren wutar lantarki ba, burin Najeriya na zama ƙasa mai tattalin arzikin dala tiriliyan ɗaya nan da shekarar 2030 na iya fuskantar cikas.

Bashin N639bn ya jefa lantarki cikin barazana

Babban manajan kasuwancin iskar gas na kamfanin Nigerian National Petroleum Development Company (NNPDC), Bashiru Adoke, ya bayyana cewa rashin ingantaccen tsarin biyan kuɗin iskar gas na daga cikin manyan matsalolin da ke kawo cikas ga samar da wutar lantarki.

Ya ce kamfanonin samar da wutar lantarki ba sa karɓar isassun kuɗaɗen da za su iya biyan kuɗin iskar gas da suke amfani da shi wajen samar da wuta.

A cewarsa, kuɗaɗen da ake samu daga kasuwar wutar lantarki ba su wadatar wajen biyan kuɗin iskar gas, duk da cewa shi ne ke cin kaso mai yawa na kuɗin da ake kashewa wajen samar da wutar.

Kara karanta wannan

Maganar zargin kisan Kiristoci ya dawo yayin da zaɓen Najeriya ke ƙaratowa

Adoke ya ce:

"Babu ingantaccen tsarin biyan kuɗin iskar gas, saboda kuɗaɗen da ake samu daga kasuwar wutar lantarki ba su isa biyan kuɗin iskar gas ba. Idan aka duba kuɗin wutar da ake samarwa a kowane wata, kusan kashi 40 cikin 100 ne ake biya, yayin da iskar gas ke cin tsakanin kashi 60 zuwa 75 cikin 100 na kuɗin samar da wutar."
Ana fargabar mutane za su koma amfani da hasken rana
Shugaba Bola Tinubu cikin tagumi yayin taro. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

'Mutane za su koma amfani da hasken rana'

Adoke ya kuma nuna damuwa kan yadda tsadar kuɗin wutar lantarki za ta iya sa mutane da kamfanoni su daina dogaro da wutar lantarkin ƙasa, su koma amfani da hasken rana da sauran hanyoyin samar da wuta da kansu.

Ya ce hakan na iya zama barazana ga dorewar tsarin samar da wutar lantarki na ƙasa.

A kalamansa:

"Ina fargabar makomar babbar hanyar samar da wutar lantarkin ƙasa, domin idan kowa ya daina amfani da ita ya koma hasken rana, ban san abin da zai rage wa wannan tsarin na ƙasa ba."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun je har gida sun harbe shugaban Miyetti Allah

Minista ya magantu kan gyaran wuta

Mun ba ku rahoton cewa Gwamnatin Tarayya ta ce an dawo da wutar lantarki a yankuna da dama da matsalar ta shafa a jihohin Legas, Ogun, Oyo, Kwara da Abuja.

An gyara layin wutar lantarki na Benin-Egbin mai ƙarfin 330kV da aka lalata, wanda ya taimaka wajen ƙara wutar da ake kaiwa Legas.

Minista Joseph Tegbe ya ce wutar da ake kaiwa yankin Legas ta haura megawatt 1,000, yayin da ake ci gaba da gyara sauran wuraren.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.