Yajin Aikin Likitoci: 'Yan Najeriya Sun Fara Kukan Tsadar Jinya a Asibitocin Kudi
- Yajin aikin kungiyar likitoci ta NARD ya fara jefa mutane marasa lafiya cikin wahala musamman masu karamin karfi
- Rahoto ya nuna cewa mutane sun fara karkata zuwa asibitocin kudi domin samun kulawa amma suna kuka kan tsadar kudin jinya
- Kungiyar NARD ta tsunduma yajin aiki ne a ranar Asabar, 1 ga watan Nuwamba, 2025 kuma ta ce ba za ta janye ba sai an biya bukatunta
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Yajin aikin da kungiyar likitoci masu neman kwarewa (NARD) ta shiga ya fara yin tasiri sosai a kan marasa lafiya, musamman masu ƙaramin ƙarfi.
Rahoto ya nuna cewa bisa tilas marasa lafiya sun fara karkata zuwa asibitocin kudi saboda babu lokitoci a asibtocin gwamnati.

Source: Twitter
Halin da marasa lafiya suka shiga
Leadership ta rahoto cewa yayin da wata mata, Grace Musa ta isa Asibitin Asokoro District Hospital da safiyar Litinin domin duba kirjinta da ke ciwo, ta taras babu likitoci.

Kara karanta wannan
Zargin kisan kiristoci: Wike ya zargi 'yan adawa da wuce gona da iri wurin yada karya
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Ban san likitoci suna yajin aiki ba. Na taho daga nesa domin na kashe kuɗin sufuri da yawa amma aka ce babu wanda zai duba ni.
"Talakawa ne kawai ke wahala. Masu kuɗi za su iya zuwa asibitocin kudi, amma mu fa ina zamu je?” in ji ta cikin kuka.
Wannan kalubale da Grace ta fuskanta, shi ne halin da dubban marasa lafiya ke ciki a fadin ƙasar nan yayin da yajin aikin ya shiga rana ta uku.
Yaushe likitoci za su koma bakin aiki?
Yayin da Kungiyar Likitoci ta NARD ta ci gaba da yajin aikin da ta fara a ranar Asabar, 1 ga Nuwamba, marasa lafiya a Lagos da kewaye sun fara fuskantar irin wannan matsala ta rashin likitoci a asibiti.
Kungiyar NARD ta ce yajin aikin zai ci gaba har sai gwamnatin tarayya ta biya bukatun mambobinta.
Wasu ma’aikatan lafiya a asibitocin kudi da na sojoji sun bayyana cewa duk lokacin da likitoci ke yajin aiki, yawan marasa lafiya da ake turawa wajensu yana ƙaruwa sosai.

Kara karanta wannan
Kiristoci: Peter Obi ya fadi matsayarsa kan yunkurin Amurka na kawo farmaki Najeriya
Sun ce suna fuskantar cunkoson marasa lafiya daga asibitocin gwamnati da ba sa aiki saboda yajin aikin, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
An fara kokawa da tsadar asibitocin kudi
Wani mazaunin yankin Anifowoshe, Ikeja, wanda ya nemi a kira shi James, ya ba da labarin cewa:
“Mun kawo maƙwabcinmu wanda ya yi hatsari. Ma'aikatan jinya sun ba shi taimakon gaggawa amma suka ce ba za su iya kwantar da shi ba saboda likitoci suna yajin aiki. Yanzu mun tafi asibitin kudi.
Wata mai jego da ta yi magana da manema labarai ta bayyana yadda yajin aikin ya shafi shawarar da ta yanke wajen zabar asibiti:
“Da safe ɗana ya fara rashin lafiya, ban wahalar da kaina wajen zuwa asibitin gwamnati ba, saboda na san su na yajin aikin.
"Kai tsaye na nufi asibitin kudi, duk da akwai tsada amma an ba shi magani kuma yanzu yana samun sauƙi.”

Source: Getty Images
Asibitin AKTH ya roki kamfanin wuta
A wani labarin, kun ji cewa asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano (AKTH), ya roƙi kamfanin raba wutar lantarki na Kano, wato KEDCO, da ya dawo da wutar lantarkin da ya yanke.
Shugabannin asibitin sun ce akwai bukatar a dawo da wutar abayan da wasu marasa lafiya da ke dogara da na’urorin taimakon numfashi suka rasa rayukansu.
AKTH ya tabbatar da cewa ana ƙoƙarin biyan duk wani bashi da ake bin asibitin domin a ci gaba da samar da kula wa ga marasa lafiya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
